Liverpool ta sayi Chiesa daga Juventus

Federico Chiesa looks on while playing for Italy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Federico Chiesa ya ci wa Juventus ƙwallo 37 jimilla
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta ɗauki ɗan wasan gefe Federico Chiesa daga Juventus ta Italiya kan fan miliyan 10.

An fahimci cewa Liverpool za ta biya ƙarin fan miliyan 2.5 idan ɗan wasan ya yi ƙoƙari sosai.

Chiesa mai shekara 26 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara huɗu, kuma shi ne na farko da mao horarwa Arne Slot ya ɗauka tun bayan isarsa filin wasa na Anfield.

Ɗan wasan na gaba na cikin taurarin da suka doke Ingila a bugun finareti na wasan ƙarshe a gasar ƙasashen Turai ta Euro 2020 da suka fafata a filin wasa na Wembley.

"Cike nake da murnar zama ɗan wasan Liverpool," kamar ya faɗa wa shafin intanet na kulob ɗin.

Lokacin da Richard Hughes ya kira ni ya ce, 'kana son ka koma Liverpool?' - shi ma kociyan ya kira ni - nan take na ce eh saboda na san tarihin wannan ƙungiyar, na san kuma yadda magoya bayanta suke ji.

"Saboda haka ina cike da farin ciki kuma na ƙagu na fara wasa."

Ya taka rawar gani a kakarsa ta farko a Juve, inda ya shiga cikin tawagar 'yan wasan Serie A mafiya hazaƙa na shekara, amma ya yi fama bayan raunin da ya ji a gwiwarsa a Janairun 2022 har ma aka yi masa tiyata.

Chiesa wanda ya buga wa Italiya wasa 51, ya ci wa Juve ƙwallo 32 cikin wasa 131, ciki har da 10 da ya ci cikin wasa 37 da ya buga a kakar da ta gabata.

Da ma kocin Liverpool Arne Slot ya ce "abin mamaki ne a ce an rufe kasuwar nan" ba tare da ƙungiyar ta sayi ɗan wasa ko ɗaya ba.

A ranar Talata ma Liverpool ta amince ta sayi golan ƙasar Georgia mai suna Giorgi Mamardashvili daga Valencia kan fan miliyan 29 - amma sai a kaka mai zuwa ya koma Anfield ɗin.