Martinez zai ci gaba da kama gola a Aston Villa kaka da yawa

Emiliano Martine

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya mai tsawo, domin ya ci gaba da gola a ƙungiyar.

Ɗan kasar Argentina, mai shekara 31, zai ci gaba da taka leda a Villa Park zuwa karshen kakar 2029.

Martinez ya koma Villa daga Arsenal kan £17m a 2020, wanda kawo yanzu ya tsare ragar Villa sama da karo 150.

Wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022 a Argentina, ya buga wasa 34 a bara a Premier League daga ciki tara ƙwallo bai shiga ragarsa ba.

Villa ta samu gurbin buga Champions League a bana, bayan da ta kare a mataki na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila da ta wuce.

Ya buga wa Argentina dukkan wasa shida da ta lashe Copa America a Amurka na biyu a jere na 16 jimilla da kasar da ɗauka.