Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙungiyoyin firimiya na bibiyar Ayyoub Bouaddi, Rulli zai bar Marseille
Everton da Leeds United da kuma Nottingham Forest na bibiyar ɗanwasan gaban Ingila mai shekara 23, Liam Delap, 23, wanda Chelsea ta sanya wa farashin £40m. (The i)
Manchester City ta yi nisa kan tattaunawa da Lille game da ɗanwasan tsakiyar Morocco mai shekara 18, Ayyoub Bouaddi, wanda ke ɗaukar hankalin Arsenal da Chelsea da Liverpool da kuma Bayern Munich. (Talksport)
Mamadou Sangare zai koma Brentford, bayan ɗanwasan Malin mai shekara 24 ya bar sansanin horon Lens a Italy. (L'Equipe - in French, subscription required)
Fulham ta kammala cinikin ɗanwasan gaban Sifaniya mai shekara 22, Gonzalo Garcia da kuma ɗanwasan tsakiya mai shekara 21, Cesar Palacios daga Real Madrid a kan kuɗi £43m. (Athletic - subscription required)
Manchester City na zawarcin mai tsaron ragar Marseille da Argentina mai shekara 34, Geronimo Rulli domin cike gurbin James Trafford. (ESPN)
Manchester United ta shirya gabatar da tayin ɗanwasan bayan Newcastle da Ingila mai shekara 21, Lewis Hall yayin da take bibiyar ɗanwasan Sifaniya da Racing Santander mai shekara 19, Jorge Salina a matsayin ko ta kwana. (Teamtalk)
Coventry City na tattaunawa da Brighton a kan mai tsaron ragar Ingila mai shekara 25, Carl Rushworth, wanda ya shafe kakar wasan bara a matsayin ɗanwasan aro a ƙungiyar.(Sky Sports)
Manchester United ta tattauna da mai tsaron ragar San Lorenzo da Paraguay mai shekara 29, Orlando Gill, kamar yadda wakilin ɗanwasan ya tabbatar. (DSports via Metro)
Ɗanwasan bayan Sweden mai shekara 19, Genesis Antwi na shirin komawa Strasbourg a matsayin aro. (Football Insider)