Ghana ta amince da ƙudurin mayar da mulkin ƙasar shekara biyar
Gwamnatin Ghana ta amince da wasu muhimman gyare-gyare da kwamitin yi wa kundin mulkin ƙasar garambawul ya gabatar, ciki har da tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa da na 'yan majalisa daga shekara huɗu zuwa shekara biyar, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin ƙasar suka ruwaito a ranar 30 ga Yuli.
Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Dominic Aniye, ya ce: "Muna tunanin waɗannan zauye-zauyen za su yi. A ƙarƙashin tsarin wa'adin shekara huɗu na yanzu, watannin farko na kowane zangon mulki suna wucewa ne wajen karɓar mulki, sannan shekarar ƙarshe ta shige cikin shirye-shiryen zaɓe."
Ya ƙara da cewa: "Wa'adin shekara biyar zai ba kowace gwamnati isasshen lokaci wajen tsara manufofi, aiwatar da su da kuma tantance sakamakonsu."
Kwamitin ya miƙa rahotonsa na ƙarshe ga Shugaba John Mahama, inda ya ba da shawarar a yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1992 kwaskwarima.
Gwamnatin ta kuma amince da wasu shawarwari da suka haɗa da:
- Ƙara yawan kujerun majalisa daga 276 zuwa 300.
- Rage mafi ƙarancin shekarun da ake buƙata domin tsayawa takarar shugaban ƙasa daga 40 zuwa 35.
Sauran shawarwarin sun haɗa da:
- Soke hukuncin kisa.
- Taƙaita yawan ministoci zuwa 60 kacal.
- Soke cikakken keɓewar shugaban ƙasa daga biyan haraji.
- Taƙaita adadin alƙalan Kotun Ƙoli zuwa 19.
- Samar da wa'adi guda ɗaya na shekara 10 ga Babban Alƙalin Ƙasa ba tare da damar sake naɗa shi ba.
Ana sa ran za a gabatar da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin nan da watan Oktoba, yayin da ake sa ran gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan sauye-sauyen a shekarar 2027.