Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko ficewar jiga-jigan NDC a Kano za ta karya lagon Kwankwasiyya?
Ana ci gaba da tattaunawa kan sabuwar ɓarakar da ake ganin ta sake kunno kai a jihar Kano, musamman bayan Sanata Rufa'i Sani Hanga ya fice daga Kwankwasiyya duk da cewa shi ne mai riƙe da babban muƙami a tsarin a yanzu.
Sanata na daga cikin ƴan majalisar dokokin Najeriya daga jigar Kano da suka ci gaba da kasancewa tare da Kwankwaso tun bayan ficewar Gwamna Abba Kabir daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
A farkon shekarar nan ne Kwankwaso da mutanensa ciki har da Sanata Hanga suka fice daga NNPP zuwa ADC, daga baya kuma suka koma NDC.
A shekarar 2023 ne aka zabi Sanata Rufai Sani Hanga a matsayin ɗanmajalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam'iyyar NNPP kwankwasiyya.
A baya-bayan nan an ga Sanata Hanga na ganawa da wasu jiga-jigan APC, ciki har da shugabanta na kasa da Gwamna Abba, a wani mataki da masu sharhin siyasa ke ganin kamar zai bar tafiyar Kwankwasiyya.
Haka kuma an ga sanatan tare da tsohon gwamnan jihar, Kabiru Gaya suna ganawa da shugaban jam'iyyar na ƙasa.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, Sanata Kabiru Gaya ya ce shugaban ƙasa ya nemi su koma APC, duk da ya nanata cewa shi ba zai yi wata magana game da abin da ya faru tsakaninsa da tsarin Kwankwasiyya ba.
Ficewar za ta taɓa lagon Kwankwasiyya?
Dr Kabiru Sa'id Sufi Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai shairhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya ce dole ficewar manyan siyasa a kusa da lokacin zaɓe ya taɓa kowace irin jam'iyya ce.
Ya ce su biyu da suka fice a yanzu ba matsayinsu ɗaya ba, inda ya ƙara da cewa dukkansu kowanne yana da yanayin nauyinsa.
"Shi Kabiru Gaya daga baya ya shiga tsarin kuma babu tabbacin irin ɗimbin magoya baya da ya tafi kamar Sanata Rufai Hanga wanda shi ne sanata ɗaya tilo da Kwankwasiyya ke da shi a Kano," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ana gani ko a kafafen sadarwa Sanata Rufai Hanga yana tara mabiya.
"Kuma a siyasa idan aka fita dole a ji ba daɗi, kuma idan aka lura dukkansu tsofaffin ƴan siyasa ne kuma suna da tasiri, musamman shi Kabiru Gaya da tsohon gwamna ne."
Masanin siyasar ya ce wannan ne ya sa fitarsu a wannan lokaci zai iya haifar da matsala ga tafiyar ta Kwankwasiyya.
"Kuma idan aka yi lakari da zaɓe na ƙara ƙaratowa, kowace jam'iyya neman ƙari take yi ba rashi ba, don haka za a iya cewa NDC ta yi rashin jiga-jigai kuma wataƙila da mabiya masu yawa."
Fita daga Kwankwasiyya
Wani abu da ake kwatantawa shi ne zubin yanayin tsarin lokacin zaɓen mai zuwa da na baya, musamman zaɓen shekarar 2019.
A game da wannan kwatancen, Kabiru Sufi ya ce akwai kamanceceniya ta hanyoyi da dama.
"Gaskiya akwai yanayi kusan iri ɗaya duba da cewa ya faru lokacin da ake tunkarar zaɓe."
Masanin harkokin siyasar ya ce a duk lokacin da aka ce zaɓe ya kusa, jam'iyyu ko tafiyar siyasa ƙari suke buƙata ba raguwa ba.
Wannan ne ya sa Kabiru Sufi yake ganin ficewar na iya taɓa ƙarfin tsarin na Kwankwasiyya.
"Wannan na iya shafar tagomashin tafiyar a idanun al'umma musamman saboda irin ƙorafe-ƙorafen wasu da suke fice, wanda kuma hakan zai iya shafar masu so su shiga saboda za su yi tunanin ba lallai su samu mafita ba saboda yawan ƙorafin masu ficewar," in ji shi.
Wani abu da wasu ke magana shi ne me ya sa ake yawan fita daga tsarin Kwankwasiyya duk da cewa ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya.
A game da wannan, Kabiru Sufi akwai yanayin tsarin tafiyar da kuma buƙatun ƴan siyasa.
"Ƴansiyasa mafi yawa idan baƙatarsu ba ta biya ba, ba dole ba ne su ci gaba da zama a tsarin da suke ciki."
Ya ce wasu suna tunanin Kwankwasiyya da ake cewa "amana tana da tsarin shugaba ne. Don haka akwai rashin fahimtar tsarin saboda tsari ne ne da ke da biyayya ga shugabanci."
Sufi ya ce a tsarin shugabancin ne wasu ke ganin wannan yanke hukuncin da shugaba yake yyi suke kallo a matsayin kama-karya.
"Musamman idan ba su samu abin da suke so ba, amma idan sun samu yadda suke so ba sa damuwa. Saboda haka ne wasu suke gani ko dai rashin fahimtar tsarin ko kuma lokacin da suka ga ba su samu abin da suke so ba ne suke tutsu," in ji shi.
Mece ce Kwankwasiyya da manufofinta?
Jaafar Jaafar babban editan Jaridar Daily Nigerian, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mai bibiyar siyasar jihar Kano ya ce Kwankwasiyyar wata aƙidar siyasa ce da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa.
Ya ce an assasa wannan aƙida ne sakamakon gwamnan jihar Kano har sau biyu da Sanata Rabiu Musa kwankwanso ya yi.
Fitaccen ɗan jaridar ya kuma ce daga cikin manufofin aƙidar sun haɗa da kare muradun talakawa, kamar yadda ƙungiyar ke iƙirari lokacin kafa ta.
''Aƙidar Kwankwasiyya ta ƙunshi duk abin da ya shafi talaka, gwamnati ta mayar da hankali kan abin da ya shafi ci gaban talakawa, musamman fannin ilimi'', in ji shi.
Jaafar Jaafar ya ƙara da cewa fannin ilimi na daga cikin muhimman fannonin da aƙidar Kwankwasiyya ta sanya a gaba.
''A tsarin Kwankwasiyya an zayyana wasu abubuwan da duk wanda ya hau mulki a kan doron Kwankwasiyya dole ne ya ba su fifiko, wato waɗanda Kwankwason ya assasa, kamar ciyar da ƴan makaranta, da ba su kayan makarantu da tura ɗalibai karatu ƙasashen waje'', in ji shi.
Kwankwaso a siyasar Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.
Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.
Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.
Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.
Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.
Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya samu kuri'u fiye da 900,000 a jihar Kano, wadda ta fi yawan ƙuri'ar da kowanne daga sauran ƴan takarar jam'iyyun suka samu a jiha ɗaya tilo, ciki kuwa har da jam'iyya mai mulki ta APC.