An raba maki tsakanin Man United da Arsenal a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan mako na 28 a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
United ce ta fara cin ƙwallo a wasan na hamayya ta hannun ƙyaftin Bruno Fernandes a bugun tazara kafin hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Gunners ta farke ta hannun Declan Rice, saura minti 16 a tashi daga karawar.
Ƙwallo na huɗu da Rice ya zura a raga a bana har da ɗaya a Champions League da Arsenal ta doke Dinamo Zagreb 3-0 ranar 22 ga watan Janairu,
Wasa na uku da suka kara a bana, bayan 2-0 da Arsenal ta ci a Emirates ranar Laraba 4 ga watan Disamba.
Sai dai United ta fitar da Arsenal a FA Cup a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci ranar 12 ga watan Janairu.
Wasannin da aka buga tsakanin Manchester United da Arsenal a bana:
Premier League ranar Lahadi 9 ga watan Maris 2025
- Man Utd 1 - 1 Arsenal
English FA Cup Ranar Lahadi 12 ga watan Janairu 2025
- Arsenal 1 - 1 Man Utd
Premier League Ranar Laraba 4 ga watan Disamba 2024
- Arsenal 2 - 0 Man Utd
Da wannan sakamakon Arsenal mai kwantan wasa ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier da tazarar maki 15 tsakani da Liverpool ta ɗaya.
Hakan na nufin Liverpool na neman maki 16 nan gaba, wato ta ci wasa biyar da canjaras ɗaya daga karawa tara da ta rage mata ta lashe kofin Premier na bana na 20 jimilla.
Ita kuma Manchester United tana mataki na 14 da maki 34 bayan cin wasa tara da canjaras bakwai aka doke ta 12.
Wannan shi ne wasa na 200 da Mikel Arteta ya ja ragama a Premier League, ya lashe karawa 118 daga ciki.
Dan kasar Sifaniya ya zama na biyar a jerin wadanda suka yi nasara da yawa a wasa 200 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Masu rike da bajintar sun hada da Pep Guardiola da Jose Mourinho da Jurgen Kloop da kuma Sir Alex Ferguson.











