West Ham ta je ta raba maki a gidan Aston Villa a Premier

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Aston Villa da West Ham sun tashi 1-1 a wasan mako na 23 a Premier League da suka buga ranar Lahadi a Villa Park.
Villa ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Jacob Ramsey a minti na takwas da take leda kuma haka suka je hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne West Ham ta farke ta hannun Emerson, saura minti 20 su tashi daga wasan.
Villa ta mamaye karawar tun kan hutu, amma hakan bai hana ƙungiyar da Graham Potter ke jan ragama kai hare-hare ba, har da wadda Lucas Paqueta ya buga ƙwallo amma ya yi faɗi.
Da wannan sakamakon Villa ta ci gaba da zama a mataki na takwas a teburin Premier League, yayin da West Ham ta yi sama zuwa mataki na 14.








