Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asensio zai koma buga wasannin aro a Aston Villa
Aston Villa na daf da ɗaukar aron Marco Asensio daga Paris St-Germain kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar nan.
Haka kuma an tsara ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford zai je a auna koshin lafiyarsa a shirin komawa buga wasannin aro a Aston Villa.
Ba a tabbatar da lokacin da za a kammala kulla yarjejeniya da ƴan wasan biyu ba, amma Villa na fatan cimma matasaya kafin a rufe kasuwar sayen ƴan wasa ranar Litinin.
A cikin watan nan na Janairu, Villa ta ɗauki Andres Garcia daga Levante da kuma Donyell Malen daga Borussia Dortmund.
Haka kuma ta sayar da Jhon Duran ga Al-Nassr mai buga gasar Saudi Arabia kan £71m da Diego Carlos da Fenerbahce ta saya kan £8.45m.
Asensio, mai shekara 29, ya ci ƙwallo bakwai a wasa 47, tun bayan da ya koma PSG daga Real Madrid a 2023, ya taka rawar da ƙungiyar ta lashe Ligue 1 a 2024.
Ya kuma taka leda a Mallorca da Espanyol, wanda ya buga wa tawagar Sifaniya wasa 38.
Ranar Asabar Aston Villa ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Wolverhampton a gasar Premier League wasan mako na 24.
Villa ta kare a matakin ƴan takwas ɗin farko a Champions League kai tsaye ranar Laraba, wadda za ta jira, domin ci gaba da zagaye na biyu wato ƴan 16.