Batutuwa biyar kan wasan Liverpool da Manchester City

An wallafa

An tashi wasa 1-1 tsakanin Liverpool da Manchester City a Anfield ranar Lahadi a gasar Premier League wasan mako na 28.

Sun raba maki a tsakaninsu kenan kamar yadda suka yi a filin Etihad ranar 25 ga watan Nuwambar 2023.

Yanzu saura wasa 10 a kammala kakar bana, Arsenal ce ta daya a kan teburi da maki iri daya da na Liverpool da tazarar rarar kwallaye.

City mai rike da kofin bara tana ta ukun teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool da kuma Arsenal.

Abubuwa da dama sun faru a wasan Liverpool da City tun daga cin kwallo da farkewa da canjin Kevin de Bruyne da VAR da kwazon da 'yan wasa suka nuna.

Ga jerin wasu batutuwa biyar kan wasan hamayya tsakanin Liverpool da City.

1. Shin ko an yi ban kwana tsakanin Klopp da Guardiola ne ?

A baya-bayan nan Premier League ta kara samun bunkasa sakamakon hamayya tsakanin Jurgen Klopp da Pep Guardiola.

Idan har wannan shi ne wasan karshe da kociyoyin suka hadu da juna to lallai ba za a manta rawar da suka taka ba a duk lokacin da suke fuskantar junansu.

Watakila su kara haduwa a FA Cup a bana - ko ma dai menene ba za a taba manta kwarewar Klopp da Guradiola ba a gasar tamaula a Ingila.

Tuni kociyan Liverpool ya sanar cewar zai ajiye aiki a karshen kakar nan, domin yana bukatar hutu ya kuma zauna tare da iyalansa.

A karawar da suka yi ranar Lahadi a zagayen farko Manchester City ta taka rawar gani wajen raba kwallo da amfani da fadin filin har zuwa cin kwallon da ta yi.

Amma daga lokacin da Alexis Mac Allister ya farke kwallon a bugun fenariti a zagaye na biyu, sai Liverpool ta karbe wasan da ya kayatar da 'yan kallo.

Ba wani koci da yake bai wa Guardiola ciwon kai kamar Klopp a duk lokacn da za su fafata da juna.

Hamayyar da ke tsakanin Klopp da Guardiola ta sa kowanne daga ciki ya kara fito da kwarewar da yake da ita a fannin horar da tamaula da lashe kofuna.

''Jurgen zai dawo fagen horar da tamaula,'' in ji Guardiola bayan da aka tashi daga karawar. ''Yana kaunar aikin matuka.'' Ya sa mun zama fitatciyar kungiya. Ya sa na kara zama kwararren koci.

''Ina fatan zai sake dawo wa nan ba dadewa, domin fannin tamaula na bukatar Klopp.''

Bayan da aka tashi wasan kociyoyin sun nuna yadda suke martaba juna ta yadda suka rungume juna kowa na yiwa juna fatan alheri.

2. Batun hukuncin VAR da Liverpool tayi fatan samun fenariti

Manchester City kan bar filin Anfield a karo da dama da cewar ko dai ba a yi mata alkalancin da ya da ce ba. Sai dai a wannan karon Liverpool ce ta yi korafi.

Lokacin da Jeremy Doku ya yiwa Mac Allister keta a gurbi mai kyau ya sa filin ya rude da cewar Liverpool ta samu damar cin kwallo na biyu.

Lamarin ya faru daf da za a tashi wasan, sai dai VAR ta fayyace ba wani laifin da aka aikata kamar yadda alkalin wasa Michael Oliver ya tabbatar, sannan 'yan dakika tsakani ya hura tashi.

3. De Bruyne bai ji dadin sauya shi da aka yi ba - amma Guardiola ya ce ba wata matsala

Karawa tsakanin Liverpool da Manchester City ta fitattun 'yan wasa ce da kowa ke fatan nuna kwarewarsa a fafatawar, kowa ya kuma gamsu da rawar da De Bruyne ya taka a wasan, ya kuma nuna bacin rai da canja shi da ka yi.

A minti na 69 aka cire dan kasar Belgium aka saka Mateo Kovacic, amma ya nuna karara bai ji dadi da Guariola ya fitar da shi ba.

Shi ne ya bugo kwanar da John Stone ya samu ya zura kwallo a ragar Liverpool, bai kuma boye fushinsa a lokacin da aka daga allon canja shi ba a wasan, wanda yake ganin ya kamata ya ci gaba da fafatawar.

Idan kace bai ji dadin canjin ba ka bata bakinka, domin lokacin da zai fita daga filin ya bude hannayensa biyu yana magana da Guardioa daga nan ya koma kan benci ya zauna.

To sai dai Guardiola ya ce ba wata matasala tsakaninsa da De Bruyne.

4. Diaz ya taka rawar gani - amma Liverpool na bukatar Salah

Lokacin da aka saka Mohamed Salah a wasa a minti na 61 magoya baya sun ji dadi da yin sowa da tafi ga dan kwallon Masar, kuma 'yan dakika tsakani da ya shiga fafatawar ya nuna amfaninsa, bayan da ya yi fama da jinya.

Taba kwallon Salah na farko ya buga tamaula mai kyau cikin kwarewa zuwa wajen Luis Diaz - shi kuwa dan kasar Colombia ya samu dama mai kyau da ya rage ya yanke Stefan Ortega, daga baya ya buga kwallon amma ta yi fadi.

Diaz ya sha mamaki da bai ci kwallon ba, ba shi kadai ba har da dukkan magoya bayan Liverpool da suke tsammanin ya kamata su hada maki uku a karawar.

5. Liverpool da Man City sun taka rawar ganin da ake bukata

Tun farko an sa ran za a yi gumurzu mai kayatarwa tsakanin Liverpool da Manchester City, kuma ba su bayar da kunya ba, domin wasa ne mai girma tsakanin wadanda ake yi a gasar Premier League.

Manchester City kan ci karo da kalubalen lashe Premier a wajen Liverpool, an samu kakar da sai a wasan karshe City ta zama zakara a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Duk lokacin da suka hadu a kan samu hamayya a tsakanin kungiyoyin biyu, musamman a Anfield, inda Guardiola ke kasa doke Liverpool.

Lokacin da alkalin wasa Oliver ya busa tashi nan take fili ya barke da tafi, hakan zai nuna maka yadda magoya baya suka gamsu da rawar da kungiyoyinsu suka taka.