Raheem Sterling zai koma Qatar domin wasan Ingila da Faransa

An wallafa

Dan kwallon Ingila, Raheem Sterling zai sake koma wa Qatar kafin ranar Asabar domin wasan kasarsa da Faransa a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan Chelsea mai shekaru 28 a ranar Lahadi ya bar Qatar zuwa Ingila bayan barayi sun shiga gidansa da ke Surrey.

Bai buga wasan da Ingila ta lallasa Senegal da ci uku da nema ba amma ana sa ran zai hade da sauran 'yan tawagar kasar a ranar Juma'a.

A wata sanarwa, 'yan sanda a Surrey na Ingila sun ce suna gudanar da bincike kan kutsawa cikin wani gidan inda aka kwashe zinare da agoguna.

Kawo yanzu babu wanda aka kama dangane da satar da aka yi a gidan Sterling.

Har yanzu hukumar kwallon Ingila - FA bata bayyana cikakken bayanin da aka yi mata ba game da kutsen.