Arsenal ta kusa kammala cinikin Gyokeres, Wissa na son komawa Tottenham

Viktor Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na daf da kammala ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden Viktor Gyokeres daga Sporting, inda Gunners din suka shirya ranar da za a gwada lafiyar ɗan wasan mai shekara 27. (Football Transfers)

Abin da ɗan wasan gaban Brentford Yoane Wissa ke so shi ne ya bi tsohon kocin Bees Thomas Frank zuwa Tottenham, duk da cewa Newcastle United ta nuna sha'awarta kan dan wasan na DR Congo mai shekara 28. (Talksport)

Everton ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz daga Juventus, yayin da Aston Villa da West Ham ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 27. (TeamTalk)

Arsenal ta nemi ɗan wasan tsakiyar Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, a farkon wannan bazarar amma ta kasa cimma matsaya da Bayern Munich. (Bild)

Wolves ta kammala cinikin ɗaukar ɗan wasan Colombia Jhon Arias mai shekara 27 daga ƙungiyar Fluminense na Brazil. (ESPN)

Nottingham Forest na aiki tuƙuru don shawo kan ɗan wasan tsakiya na Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 25, ya kulla yarjejeniyar dogon zango a kulob ɗin, sakamakon ƙaruwar sha'awar da Tottenham ke nunawa kan ɗan wasan. (Givemesport)

Leeds United na tattaunawa kan sayen ɗan wasan Feyenoord mai shekara 25 ɗan ƙasar Brazil Igor Paixao. (Sky Sports)

West Ham na tattaunawa da ɗan wasan baya na Ingila Kyle Walker-Peters, mai shekara 28, wanda ya zama ɗan wasa mai zaman kansa bayan ya bar Southampton ya kuma ƙi amincewa da tayin Besiktas. (Talksport)

Inter Milan ta miƙa tayin ɗaukar aron ɗan wasan gaba na Najeriya Ademola Lookman tare da alƙawarin biyan fam miliyan 34.6 na siyan dan wasan a bazara mai zuwa amma Atalanta ta yi watsi da wannan tayin inda ta ke son fam miliyan 43.2 kan ɗan wasan mai shekara 27. (Sky Sports Italia)

Luton Town na shirin ɗaukar golan Jamhuriyar Ireland Josh Keeley daga Tottenham bayan ɗan wasan mai shekara 22 ya kasa amincewa da sabon kwantiragi da Spurs. (Standard)

Ɗan wasan Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 20, yana tattaunawa don komawa Roma a wannan bazarar. (Fabrizio Romano)