Arsenal ta nace kan Sterling, Osimhen zai tafi Saudiyya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na diba yiyuwar yadda za ta ɗauko ɗanwasan gaba na Chelsea da Ingila mai shekara 29 Raheem Sterling ko kuma ɗanwasan gaba na Bayern Munich da Faransa Kingsley Coman, mai shekara 28 kafin rufe kasuwar ƴanwasa. (Independent)

Newcastle za ta haƙura da ɗanwasan da ta daɗe tana farauta Marc Guehi, mai shekara 24, bayan ta gaji da jan ran Crystal Palace. (Sky Sports)

Ɗanwasan gaba na Ingila da Brentford Ivan Toney, mai shekara 28, ya shiga rashin tabbas kan makomarsa yayin da lokaci ke ƙurewa. (Mirror)

Kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya tana dab da ɗaukar ɗanwasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25, yayin da take ƙoƙarin shan gaban Chelsea. (Talksport)

Liverpool ta yi watsi da tayin kuɗi haɗi da ɗanwasan Nottingham Forest kan golanta na Jamhuriyyar Ireland Caoimhin Kelleher. (Athletic - subscription required)

Chelsea na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan gaba na Ingila Jadon Sancho, mai shekara 24, amma ta ba Manchester United sharuɗɗa kafin ɗaukar ɗanwasan. (Teamtalk)

Fulham ba za ta ɗauko ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Paraguay ba mai shekara 30 Miguel Almiron. (Mail)

Ɗanwasan baya na West Ham da Faransa Kurt Zouma, mai shekara 29, an kammala diba lafiyarsa bayan ya koma Al-Orouba ta Saudiyya a matsayin aro. (Sky Sports)

Chelsea ta tuntuɓi Benfica kan ɗawasan bayanta Tomas Araujo mai shekara 22. (Mirror)

Brighton ta taya ɗanwasan gaba Nordsjaelland Conrad Harder mai shekara 19 kan fam miliyan 17.

Fulham na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan gaba na Lille da Kosovo Edon Zhegrova, mai shekara 25, kafin rufe kasuwar ƴanwasa. (Football Insider)