Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Napoli ta ɗauki Lukaku daga Chelsea
Ƙungiyar Napoli ta Italiya ta kammala ɗaukar Romelu Lukaku daga Chelsea kan fan miliyan 30.
Kociyan Napoli Antonio Conte ne ya dage kan sayen Lukaku mai shekara 31, wanda a ƙarƙashinsa ne ɗan wasan ya taka rawar gani a kaka biyu da suka yi tare a Inter Milan daga 2019 zuwa 2021.
Ɗan wasan gaban ya sake komawa Chelsea a 2021 kan fan miliyan 97.5 amma kuma ya shafe kaka biyu da suka wuce yana taka leda a Italiya a matsayin aro - farko a Inter, daga baya kuma a Roma.
Lukaku ya ci ƙwallo 24 lokacin da ya lashe gasar Serie A a ƙarƙashin Conte a 2021, inda daga nan ne kuma ya ja hankalin Chelsea.
Rabuwa da ɗan ƙasar Belgium ɗin - wanda bai buga wa Chelsea wasa ba tun watan Mayun 2022 - za ta taimaka wa kulob ɗin daina biyan albashinsa da ya kai fan 235,000 duk mako.
Da yake magana yayin taron manema labarai, Conte ya ce Lukaku zai iya buga wasansa na farko ranar Asabar da za su fafata da Parma.
A gefe guda kuma, Chelsea na cigaba da tattaunawa domin sayen ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen mai shekara 25, wanda zai taimaka wa Napoli rage abin da ta kashe kan Lukaku.
Ita ma Al-Ahli ta Saudiyya na son ɗan wasan gaban na Najeriya.