Ikorodu City ta doke Kano Pillars a Premier ta Najeriya

Ikorodu City

Asalin hoton, Ikorodu fc Twitter

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ikorodu City ta doke Kano Pillars 4-1 a wasan mako na 20 a gasar Premier ta Najeriya da suka kara ranar Laraba a Legas.

Ikorodu City ta fara cin ƙwallo a minti na biyu da take leda ta hannun Adelani Shola, sannan ta kara na biyu ta hannun Uzondu Harrison a minti na 27.

Daf da za su je hutu ne Pillars ta zare ɗaya ta hannun Abba Adam, kuma na huɗu da ya zura a raga a kakar nan.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne mai masaukin baƙi ta kara na uku, bayan da Pillars ta ci gida a kwana daga Harrison Austin, sannan Ayomide Cole ya ci na huɗu.

Tun a ranar Talata da sanyin safiya Pillars ta ziyarci Legas a jirgin sama a karon farko da gwamnati ta yi wannan bajintar a kakar nan.

Ta kuma yi haka ne domin ƴan wasa su samu natsuwa da hutun da suke bukata, domin buga wasa da Ikorodu, sannan su koma Kano a kan kari don fuskantar wani kalubale ranar Lahadi.

Ranar 8 ga watan Satumba, Pillars ta caskara Ikorodu City 3-0 a wasan farko na fara kakar bana da suka fafata a filin wasa na Muhammadu Dikko a jihar Katsina.

Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu, Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Bayelsa United, ita kuwa Ikorodu City za ta je Enugu Rangers.

Wasu daga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Akwa United 1-1 Lobi Stars
  • Remo Stars 3-2 Abia Warriors
  • Shooting Stars 1-0 Nasarawa United
  • Bayelsa United 4-1 Sunshine Stars FC
  • El-Kanemi Warriors 2-1 Rangers International