Cristiano Ronaldo ya zama mai shirya finafinai

Asalin hoton, Getty Images
Tauraron ɗanwasa Cristiano Ronaldo ya fantsama harkar shirya finafinai tare da haɗin gwiwar kamfanin UR-Marv da suka kafa tare da mai bayar da umarni Mathew Vaughn.
Wannan yunƙuri nasa ya tabbatar da sha'awar fara sabuwar sana'a da ɗan ƙasar Portugal ɗin mai shekara 40 ya bayyana a baya da cewa "harka ce da ke burge ni yayin da nake neman shiga wasu harkokin kasuwnacin".
Wata sanarwa da Ronaldo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce tuni suka shirya zango biyu na wani fim tare da Vaughn, wanda za a fitar da bayanai kansu nan gaba, har ma sun fara aiki kan zango na uku na fim ɗin.
Matthew Vaughn sananne ne a masana'antar, inda ya shirya finafinai "Kick-Ass" da "Kinsman", kuma ya ce ya zaƙu game da haɗakar tasu da Ronaldo.
"Cristiano ya samar da labarai yayin da yake taka leda waɗanda ban taɓa tunani ba. Muna da zimmar ƙayatar da 'yankallo tare da shi," kamar yadda sanarwar ta ambato shi yana faɗa.
Baya ga shigarsa harkar fim, Ronaldo na ci gaba da faɗaɗa harkokinsa a wajen wasanni.
Ya zuba jari a kafar yaɗa labarai ta Portugal mai suna Medialivre da kuma kafa tasharsa ta YouTube mai suna UR Cristiano a 2024, yayin da yake son cigaba da ɗaukaka sunansa a duniya.







