Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ake la'akari da shi wajen bayar da lambar yabo a Najeriya?
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A Najeriya 'yan ƙasar da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan ƙorafin da majalisar wakilan ƙasar ta yi kan rashin nuna daidaito dangane da lambobin yabon da aka bai wa shugabanta da na majalisar dattawan ƙasar.
A jawabinsa na ranar bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun 'yancin kai, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanar da bayar da lambobin yabon da wasu jagororin ƙasar, ciki har da kakakin majalisar wakilan da aka bai wa lambar yabo da CFR, yayin da aka bai wa takwaransa, na majalisar dattawan ƙasar lambar yabo ta GCON.
Wani mataki da bai yi wa 'yan majalisar wakilan daɗi ba, waɗanda suka yi watsi da lambar karramawar.
'Yan majalisar sun ce matakin nuna bambanci ne tsakanin majalisun ƙasar biyu waɗanda suke ce ''a ƙa'ida babu wani bambanci tsakanin majalisun biyu''.
Wannan batu dai ya haifar da muhawara, tsakanin 'yan ƙasar, inda wasu ke tambayar abin da shugabannin majalisar biyu suka yi, da har suka cancanci a ba su lambar yabo ta karramawa.
Mece ce lambar yabo ta karramawa?
Barista Audu Bulama Bukarti wani ƙwararren lauya ne mai sharhi kan al'amuran yau da kullum da ke zaune a Birtaniya, ya ce lambar karramawa, wata lambar yabo ce da ake bai wa wasu mutane da suka ƙere sa'a ko zarra ta fuskar hidimta wa ƙasa.
''Hidimtawar za ta iya kasancewa a aikin gwamnati ko kasuwanci, ko kafa wani kamfani domin ƙera wasu abubuwa da ƙasa za ta amfana da su, da bai wa mutane aikin yi, ko shugabannin al'umma ko malamann addini, ko wani ɗan gwagwarmaya da ya yi fice wajen kare haƙƙin al'umma'', in ji Bukarti.
Ya ƙara da cewa babban abin da ake so shi ne a ce mutum ya yi fice a wani abu na hidimta wa ƙasa, ko hidimta wa wasu mutane a cikin ƙasar.
Ya ci gaba da cewa wani rukunin mutanen da ake bai wa irin waɗannan lambobi sun haɗa da sojojin da suka nuna zaƙaƙuranci a aikinsu na yaƙi da 'yan bindiga a cikin ƙasa, da kuma mkiya ƙasa daga waje.
Daga ina Najeriya ta koyo bayar da lambar?
Barista Bukarti ya ce Najeriya ta samo wannan al'ada ta karrama mutane da lambar yabo, daga ƙasar Birtaniya wadda ta yi mata mulkin mallaka.
''A nan Birtaniya za ka ga wanda ke matsayin Sarki ko Sarauniya a tarihi na ƙoƙarin karrama mutanen da suka yi fice a ƙasar da lambobin yabo irin su OBE da MBE da CBE da sauransu'', in ji Lauyan.
Haka ma a Amurka ana bayar da irin waɗannan lambobi na yabo, waɗanda shugaban ƙasa ke bai wa mutanen da majalisar dokokin ƙasar ta amince a ba su.
Manyan lambobin yabo takwas a Najeriya
Barista Bukarti ya ce a Najeriya akwai manyan lambobin yabo takwas da aka fi bayar da su.
Lambar yabo mafi girma a Najeriya ita ce GCFR da galibi aka ware ta ga shugaban ƙasar kaɗai.
''Galibi akan bai wa shugaban ƙasa lambar yabo ta GCFR tun daga ranar da aka rantsar da shi a kan mulki, inda za a riƙa maƙalata a gaban sunansa, wasu kuma sai sun sauka ake ba su , wasu ma sai bayan mutuwarsu ake ba su wannan lamba'', in ji ƙwararren lauyan.
Ya ƙara da cewa baya ga wannan lamba a ƙasa da ita akwai sauran manyan lambobin yabo da suka haɗa da GCON, wadda galibi ake bai wa mataimakin shugaban ƙasa da manyan-manyan alƙalan kotun ƙoli da sauran manya-manyan ma'aikatan gwamnati na sama-sama can.
Sannan kuma akwai lambar yabo da CFR da ke bi musu, da galibi ake bai wa manyan-manyan sarakunan gargajiya.
Ga jerin lambobin yabon takwas da ake karrama mutane da su a Najeriya.
- Grand Commander of the Order of the Federal Republic (GCFR)
- Grand Commander of the Order of the Niger (GCON)
- Commander of the Order of the Federal Republic (CFR)
- Commander of the Order of the Niger (CON)
- Officer of the Order of the Federal Republic (OFR)
- Officer of the Order of the Niger (OON)
- Member of the Order of the Federal Republic (MFR)
- Member of the Order of the Niger (MON)
Bukarti ya ce ana bayar da waɗannan lambobi ne dangane da irin hidimtawar da mutum ya yi a ƙasar
Wace cancanta ake bi wajen bayar da lambar?
Barista Audu Bulama Bukarti ya ce akwai wani kundin doka da aka yi, mai suna 'National Honours Act' wadda aikinsa shi ne kula da yadda za bayar da waɗannan lambobin yabo na karramawa.
''An yi wannan doka a shekarar 1964, kuma dokar ta ware ire-iren lambobin karramawa da za a bayar da kuma irin mutanen da suka cancanta a ba su lambar yabo a Najeriya'', in ji Barista Bukarti.
Ya ƙara da cewa dokar ba ta fayyace wata takamammiyar ƙa'ida wadda za a yi la'akari da ita don bayar da ita ba.
Sai dai kawai ta ce duk wanda ya yi fice ko zarra ko ya kere sa'a a wani fanni na ciyar da ƙasa gaba, to ya cancani samun lambar.
Rukunin mutanen da ake bai wa lambar yabon
Barista Bukarti ya ce ba a ware wasu rukunin mutanen takamaimai domin ba su lambar yabon ba, sai dai ana bayar da ita ne ga duka rukunin mutanen da suka yi fice a fannoni daban-daban na gina ƙasa.
Rukunin mutanen da ke samun waɗannan lambobi sun haɗa da:
- Jagororin al'umma
- Sojoji
- Manyan ma'aikatan gwamnati
- Malamai na Boko da na addini
- Marubuta
- Lauyoyi
- Masu bincike
Babban maƙasudin shi ne don a zaburar da sauran 'yan ƙasa su ma su yi azamar yin wani abu na gina ƙasa.
Yadda ake zaɓo mutanen da za a karrama da lambobin
Yadda ake yi wajen zaɓo mutanen da za a karrama shi ne akan bai wa manya-manyan jami'an gwamnati ko shugabannin hukumomi da gwamnatocin jihohi dama su zaɓo mutanen da suke ganin sun cancanta su samu waɗannan lambobin yabo.
Bayan sun zaɓo sunayen, za a tura wa kwamitin bayar da lambobin yabon, wanda kuma shi ne zai tace sunayen, ya zubar da wasu ya kuma tantance wasu.
''Daga nan sai kwamitin ya aike da sunayen wajen shugaban ƙasar, wanda shi kuma zai saka hannu kan sunayen da yake ganin sun cancanta a ba su lambobin, domin shi ne doka ta bai wa damar bayar da lambobin'', in ji Bukarti.
Za a iya ƙwace lambar yaɓo daga hannun wani?
Ƙwararren lauyan ya ce dokar ta bai wa shugaban ƙasa damar ƙwace lambar a hannun duk mutumin da aka ba shi ita, amma daga baya aka same shi da wani laifi na assha, kamar cin amanar ƙasar, ko cin hanci da rasahawa.
''Dokar ta bai wa shugaban ƙasa damar ƙwace lambar idan aka samu mutum da aikawa wani abu na cin amanar ƙasa'', in ji Lauyan.