Liverpool na zawarcin Gyokeres, Chelsea ta kusa daidaitawa da Gittens

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta bi sahun Manchester United da Arsenal a zawarcin ɗanwasan Sporting mai shekara 27 Viktor Gyokeres. (Correio da Manha - in Portuguese)
Chelsea ta kusa ƙulla kwantiragi da ɗanwasan Borussia Dortmund da Ingila ɗan ƙasa da 21 Jamie Gittens mai shekara 20, yayin da ƙungiyar ta Bundesliga ke fatan samun shi kan fam miliyan 50. (ESPN)
Manchester United na iya amincewa da tayin fam miliyan 45 don ta samu cefanar da ɗanwasan Argentina mai shekara 20 Alejandro Garnacho. (Star)
Newcastle na ƙyalla ido kan ƴanwasa irin su Johan Bakayoko mai shekara 23 da ke buga wa PSV Eindhoven da Belgium da ɗanwasan Borussia Dortmund da Jamus, Kerim Adeyemi mai shekara 23 idan haƙarsu ba ta cimma ruwa ba a ƙoƙarinsu na ɗauko ɗanwasan Nottingham Forest da Sweden Anthony Elanga mai shekara 23. (Teamtalk)
Manchester United na fuskantar ƙalubalen sayar da ɗanwasan Netherlands Tyrell Malacia mai shekaa 25 wanda ya taimaka wa PSV Eindhoven lashe kofin Eredivisie yayin da yake zaman aro a kakar da ta wuce. (Athletic - subscription required)
Sunderland ta tattauna da Nice kan yarjejeniyar da ta shafi golan Poland mai shekara 25, Marcin Bulka. (Fabrizio Romano)
Everton ta soma tattaunawa da Villareal na La Liga kan ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan gaba na Faransa mai shekara 22 Thierno Bary kuma ba su yanke ƙauna da biyan fam miliyan 34 ba na tanadin kwantiragin. (ESPN)
Manchester United ta yi watsi da tayin fam miliyan 6.5 daga Hoffenheim kan ɗanwasan Ingila ɗan ƙasa da shekara 21 Callum Doyle. (Mail)
Everton na ci gaba da fatan sayen ɗanwasa Kenny Tete duk da rahotanni da ke cewa Fulham ta yi wa mai shekara 29 ɗin ɗan asalin Netherlands tayin sabunta kwantiraginsa. (Independent, external)
Har yanzu Benfica ba ta samu tayi daga Real Madrid ba bayan da aka alaƙanta kulob ɗin da neman Alvaro Carreras mai shekara 22, wanda a bara, daga Manchester United ya koma Lisbon. (Marca - in Spanish)












