Europa : Man Utd na dari-dari - Amorin

 Ruben Amorim
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Manchester United Ruben Amorim yana dari-dari a kan wasan da za su yi na gasar Europa - Alhamis din nan da dare (09:00 agogon Najeriya).

Amorin ya sha jinin jikinsa ne a lokacin taron manema labarai da ya yi kan wasan da za su yi da Rangers kan tambayar da aka yi masa a game da yadda kwazon kungiyar a yanzu kasancewar a gidanta -Old Trafford za ta yi wasan.

A kan hakan ne ya ce suna dari-dari a duk lokacin da suke wasa a gida a yanzu sabanin a waje - kuma lamarin na kara zamar musu mai wuyar gaske.

''Gaskiya nake fada ba na son na yi kauce-kauce na fadi wani abu daban - yadda lamarin yake kenan a zahiri,'' in ji shi.

An doke Manchester United a wasa hudu da ta yi cikin biyar na Premier a Old Trafford.

Kuma rashin nasara da kungiyar ta yi guda shida a wasanninta na farko na gida a gasar Premier, shi ne mafi muni tun kakar 1893-94.

Ita kuwa Rangers ba a doke ta ba a wasanta biyar na baya-bayan nan a dukkanin gasar da ta yi

A wasa hudu na gasar Premier ta Scotland ta yi canjaras da Hibernian da Dundee sannan ta doke St Johnstone da kuma Aberdeen.

Sannan a wasan cin kofin kalubale na Scotland (Scottish Cup) ta doke Fraserburgh 5-0.

Damar kungiyoyin biyu a gasar ta Europa

A yadda al'amura suke dukkanin kungiyoyin biyu na iya samun tsallakawa zuwa zagaye na gaba na sili-daya-kwale a gasar ta Europa.

United na matsay na bakwai da maki 12 yayin da ya rage mata wasa biyu na rukuni.

To amma fa teburin a cakude yake inda Elfsborg ke matsayi na 25 da maki bakwai saboda haka akwai yuwuwar daya daga cikinsu ko kuma su biyu Manchester United ko Rangers din su fadi gaba daya.

Matakin samun gurbin zagayen gaba na gasar kai-tsaye ya kare ne daga matsayi na takwas, saboda haka dukkanin kungiyoyin biyu koeacce za ta yi kokarin ganin ta zama a saman teburin.