Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Gara na mutu a Lebanon da na koma Najeriya'
- Marubuci, Foluke Ogunbayo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Idan gwamnatin Najeriya ta tura jirgin sama domin kwashe jama'arta daga Lebanon a yau, galibin ƴan Najeriya ba za su shiga jirgin ba.
Wasu ƴan ƙasar a Lebanon sun shaida wa BBC cewa sun gwammace su zauna har ma su mutu maimakon su koma gida, suna masu cewa za su yi amfani da damar da suke da ita a Lebanon ɗin da a yanzu take fuskantar hare-haren Isra'ila, a maimakon su koma Najeriya inda ba su da tabbas kan makomarsu, ga kuma matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki.
Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ya shaida wa BBC ranar Juma'a cewa mutum 70 ne kawai suka yi rajistar a kwashe su cikin ƴan Najeriya 2,000 da aka san suke zaune a Lebanon.
Kakakin ya ce: "Ba za a fara kwashe mutane ne ba har sai an samu adadin mutanen da za su cika jirgin."
A wata sanarwa da tun farko aka fitar, ma'aikatar ta ce mutum 500 ne suka nuna suna son a mayar da su Najeriya.
“Iyayena da ke Najeriya ba su da lafiya, wa zai kula da su, wa zai biya basukan a Najeriya? Gwara na mutu a nan da a ce na koma Najeriya," in ji Adeola, wadda ta kasance ƴar'aiki a Beirut.
Adeola, ƴar shekara 25 a duniya ta kasance a Libenon tsawon shekaru biyar, inda take a matsayin ƴar'aiki a wani gida na ƴan Lebanon da suka tsere bayan da hare-haren Isra'ila suka ta'azzara.
Iyayen gidanta sun tafi sun bar ta lokacin da wani baƙin hayaƙi ya lulluɓe kudancin wani yanki a Beirut, babban birnin Lebanon yayin da bama-bamai suka riƙa fashewa a wurare daban-daban.
Sun yi alƙawarin su ci gaba da biyanta albashinta dala 300 matuƙar ta ci gaba da zama don kula da gidansu. A ƴan kwanakin nan, ba ta da tabbacin irin kusancin da hari na gaba zai yi da gidan da a yanzu aka ɗaɗe domin ta kula da shi.
Sai dai basussukanta da tarin kuɗin maganin kula da iyayenta da sauran buƙatunta a Najeriya na nufin a wajenta, batun komawa gida bai taso ba ma.
Yayin da Isra'ila ta zafafa hare-hare kan Lebanon domin murƙushe mayaƙan Hezbollah, ƙasashen duniya sun buƙaci jama'arsu da su fice daga ƙasar. Gwamnatin Najeriya ita ma ta bi sahu wajen sanar da tsarin kwashe jama'arta.
Duk da cewa iyayen gidansu sun tsere tare da barin su da ƙarar musayar wuta da na bama-bamai da karakainar mutane da ke neman tsira, ga wasu ƴan Najeriya, komawa gida ba ta taso ba.
Akasarin ƴan Najeriya da ke zaune a Lebanon sune ke ɗaukar ɗawainiyar iyalinsu da ke gida kuma ba za su iya komawa ba su ƙara zama nauyi ga iyalansu, kamar yadda Rowland Aigbovbiosa, shugaban ƙungiyar yan Najeriya da ke Lebanon ya shaida wa BBC.
"Yanayin da Najeriya ke ciki kwata-kwata ba na koma wa bane," in ji shi.
Mista Aigbovbiosa ya kuma ce mutane da yawa na ganin akwai yiwuwar nan kusa a cimma zaman lafiya tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi kuma akasarin ƴan Najeriya da a yanzu suke da gwaggwaɓan ayyukan yi a Lebanon suna da fatan za a samu zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa wasu na fargabar cewa ba za su sake samun damar dawowa ba idan suka bar Lebanon kuma suka ji suna son su koma bayan yaƙin.
Joy, ita ma wata ƴar Najeriya da ta daɗe tana aiki a matsayin ƴar'aiki a wani gidan ƴan Lebanon, ta faɗa wa BBC cewa ba ta shirya komawa ba. Dalili kuwa shi ne saboda hidindimunta a Najeriya inda ta ce babu yiwuwar ta samun aiki mai gwaɓi a can.
"Babu wanda yake son samun kansa a yanayin zaɓar tsakanin zama a cikin yaƙi (a ƙasar waje) da komawa ƙasarsu ta asali. Amma ba zan yi gaggawar komawa Najeriya ba inda gwamnati ba ta da tallafin da za ta yi mana," in ji ta.
Ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki a Najeriya da faɗuwar darajar naira da rashin aikin yi da ƙaruwar talauci, sun sa ƴan Najeriya neman tsira a ƙasashen waje.
A yanzu, Akinbobola, wata ƙwararriya kan nazarin bayanai da a yanzu take aiki a Lebanon a matsayin ƴar'aiki ta buɗe wani dandalin WhatsApp don jin ɗuriyar ƴan Najeriya don kowa ya san halin da kowa ke ciki. Dandalin yana kuma samar da ƙarin bayanai kan halin da ake ciki da kuma wuraren tsira.
Ita ma ba za ta iya barin Lebanon ba a wannan lokacin saboda ƙannenta uku da ke gida Najeriya sun dogara ne a kanta. Barin aikinta a Lebanon na iya kawo ƙarshen karatun ƙannenta. Kuma a cewarta, abu mafi muni shi ne ganin kanta a matsayin ƙarin nauyi ga iyalinta da ke fama da rayuwa idan ta koma gida a yanzu.
A cewar hukumar kula da ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje, babu wani ɗan Najeriya da ya ji rauni ko kuma ya rasa ransa tun soma yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah amma ta shawarci ƴan Najeriya da ke zaune a yankunan da aka mamaye da su koma wasu yankunan Lebanon da suke da tsaro.
"Duk da cewa galibinsu ba su nuna sha'awar komawa gida ba duk da kwaɗaitar da su da ofishin jakadancinmu yake, za mu ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin tabbatar da tsaron al'ummarmu," kamar yadda yake cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana.