Tsaka mai wuyar da ƴan Gaza suke ciki game da makomarsu

    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hoton da aka ɗauka ta sama na yankin Jabalia yana da ɗaga hankali. Da gani za ka ga garin yana kama da yadda Hiroshima ya ɗaiɗaice. Baraguzan gidaje ne kawai za ka riƙa gani, wasu a tsaye, wasu sun rusuna.

Yadda garin ya lalace ne ya sa zai yi wahalar gaske a iya kwatanta shi da yadda yake idan aka tuno da yadda yake cike a baya.

Amma duk da haka, jirage masa matuƙa su ɗauko wasu hotunan ƙananan tantuna da mutane suka kafa suna zama a ciki.

Bayan sama da mako shida da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yanzu rayuwa ta fara komawa yadda take a baya a Jabalia.

A unguwar al-Qasasib, Nabil ya koma wani bene mai hawa huɗu, wanda abin mamaki har yanzu yana nan daram, duk da cewa babu tagogi da ƙofofi - wasu bangunan ma sun lalace.

"Kalla yadda garin ya wargaje," in ji shi a lokacin da yake zagayawa cikin Jabalia.

"Suna so ne mu bar garinmu ba tare da an sake ginawa ba? ta yaya za mu bar garin nan. Mafi ƙarancin abin da za mu iya yi shi mu tsaya mu sake gina garin domin yaranmu."

Yanzu Nabil na amfani ne da murhu da itace da yake ajiyewa a matakalar hawa benen domi yin girki.

A wani ɓangaren benen ne Laila Ahmed Okasha take wanki ya shanya.

"Babu ruwa, babu wutar lantarki da hanyar ruwa," in ji ta, sannan ta ƙara da ta cewa, "idan muna buƙatar ruwa, muna tafiye ne mai nisa kafin mu ɗebo ruwa a bukiti."

Ta ce ta yi kuka sosai a lokacin da ta dawo ta ga yadda gidajensu suka ɗaiɗaice.

Ta zargi Isra'ila da Hamas da tarwatsa garin. "Su ne suke illata mana garin. A baya mun yi rayuwa cikin jin daɗi da walwala."

Bayan ɓarkewar yaƙin a Oktoban 2023, Isra'ila ta shaida wa mutanen yankin Falasɗinu a arewacin Zirin Gaza - ciki har da Jabalia - cewa su koma yankin kudu domin su tsira da ransu.

Dubban mutane sun ji shawarar, suka bar yankin, amma wasu da dama suka ƙi ji, inda suka zaɓi cigaba da zama.

Da Laila da mijinta Marwan sun cigaba da zama a garin har sai a watan Oktoba, lokacin da sojojin Isra'ila suka sake faɗa wa Jabalia, bayan sun ce sun gano Hamas na sake taruwa domin cigaba da yaƙi.

Bayan wata biyu suna rayuwa a sansanin gudun hijira na Shati, Laila da Maryam sai suka koma Jabalia, suka samu garin ya ɗaiɗaice.

"Da muka koma muka ga yadda aka tarwatsa mana gida, sai na ji ba na son cigaba da zama a garin," in ji Marwan.

"Na ji daɗin rayuwa a nan a baya, amma yanzu ji nake tamkar a jahannama nake. Idan na samu damar tafiya wani wurin, zan tafi."

Tsayawa ko tafiya? yanzu makomar mutanen Gaza ita ce babbar abar tattaunawa a duniya.

A watan Fabrairu, Donald Trump ya bayar da shawarar cewa Amurka za ta ƙwace Gaza, sannan kusan mutum miliyan biyu na yankin Falasɗinu su bar yankin su koma wasu wuraren.

Sai dai bayan suka da ya sha daga ƙasashen Larabawa, daga baya Tump ya ɗan janye maganar, inda ya ce shawara ya bayar, amma ba zai tilasta kowa ba.

Daga yunƙurin da Masar ta shige gaba wajen fafutikar tabbatarwa, tana so mutanen ƴankin Falasɗinu su cigaba da rayuwa a Gaza a daidai lokacin da ake sake gina yankin.

Haka kuma yunƙurin Donald Trump ya sake fito da taurin kan mutanen Gaza.

"Idan Trump na so mu tafi, ni zan cigaba da zama a Gaza," in ji Laila. "Na fi so in tafi da kaina, amma ba zan bar Gaza saboda shi ba."

A wani titin, akwai wani bene mai hawa tara, amma duk da yadda aka tarwatsa ginin, akwai mamakin yadda bai faɗi ba.

Sai dai saman benen ya lalace, wanda hakan ya sa ake fargabar dole nan gaba a rushe ginin baki ɗaya, amma duk da haka wasu mutane da dama na cigaba da rayuwa a gidan.

Shagon kayan kwalliya na Sanaa Sanaa Abu Ishbak.

Mai shekara 45 ce, wadda take da ƴaƴa 11, da ta fara sana'ar kayan kwalliya shekara biyu kafin yaƙin ya ɓarke, amma dole ta tsere ta bar sana'ar ta koma kudancin yankin a watan Nuwamban 2023.

Ta koma garin bayan an sanar da yarjejeiyar tsagaita wuta tare da mijinta da ƴaƴanta. Tuni ta fara share-share a shagon, tare da ƙoƙarin gyara shagon domin ta koma ta cigaba da harkokinta.

"Ina son sansanin Jabalia," in ji ta, "kuma ba zan bar garin nan ba sai na mutu."

Da Sanaa da Laila suna da ƙarfin gwiwar cigaba da zama a gaarin matuƙar za su iya.

"Ko rubuta sunanta ba za ta iya rubutawa ba," in ji Laila da take magana game da kakarta.

"Babu hanyoyin samun ilimi a Gaza."