Me ya sa gemu ke fito wa wasu matan?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Idris
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da a tsari na halitta maza kawai aka sani da gashin gemu ko na baki ko kuma na ƙirji, wasu lokutan akan samu wasu tsirarun matan da ke da irin gashin.
Hakan ta sa wasu ke ɗiga ayar tambayar shin fitowar gashi irin na maza a fuska ko wasu sassan jikin mace matsala ce, ko kuwa dai halitta ce kawai?
Dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi Dr Sadiya Musa Gwadabe ƙwararriyar likitar mata a ɓangaren Obstetrics and Gynaecology ta asibitin koyarwa na Illorin da ke jihar Kwara domin jin ƙarin bayani.
Me ya sa irin wannan gashi ke fito wa wasu matan?
A cewar Dr Sadiya, dalilin da ya sa gashi ke fito wa wasu mata a wuraren da galibi maza aka fi sani da su shi ne, hakan na faruwa ne idan aka samu wani sinadari mai suna Androgen wanda kuma ake kira Testosterine ya yi yawa a jikin mace.
"Duka mata da maza na da wannan sinadarin. Amma na maza ya fi na mata yawa, shi ya sa idan aka samu wannan Testosterine ɗin ya yi yawa a jikin mace ake samun fitowar gashi a wurare irin na maza kamar a gemu, ko kewayen baki, ko ƙirji ,ko a ciki da sauran wurare," a cewar likitar.
Ana kiran lalurar da suna Hirsutism a Turance.
Cuta ce ko kuwa?
Ya danganta da inda gashin ya fito.
Likitar ta ce fitowar gashi a fuska da wasu sassa na jiki ba ciwo ba ne, yayin da a waɗansu kuma ciwo ne.
"Dalilin da ya sa na ce haka shi ne, wasu lokutan idan aka duba wasu matan masu irin gashin ba a gano wani dalili, irin wannan yanayin ake kira da Idiopathic - wato an rasa dalilin fitowar gashin," in ji likitar.
Sai dai akan samu dalilin faruwar hakan a tattare da wasu matan kamar haka:
- Matsalar gaza fitar da ƙwai, inda za a ga wasu matan na fuskantar matsalar ɗaukar ciki da wuri.
- Ƙwayayen na iya zama kansa wato cutar daji a wurin da ta sa gashin ke fita. Wani lokacin ma akwai masu ciki da za a ga hakan na faruwa da su.
- Sannan matan ba su yin al’adarsu akai-akai. Sukan yi wata uku ko fiye ba su zubar da jinin al’adarsu ba.
- Sannan za a ga gashin yana fito musu a fuska.
Me ke haifar da larurar Hirsutism?
A cewar likitar, akwai wata cuta da ake kira da Polycystic Ovarian Syndrome (POS).
"Idan mace ta samu matsala a gidan ƙwai da yake fitar mata da ƙwayaye duk wata - wanda daga shi ne take ganin al’adarta - idan ciki bai samu ba yana iya fuskantar matsala.
"Shi ya sa idan mace na da wannan lalurar za ta iya fitar da gashi a fuskarta, ko a ciki ko kuma a ƙirji."
Ta yaya mace za ta iya gane tana ɗauke da Hirsutism?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Sadiya ta yi bayanin cewa mata masu irin wannan na fuskantar rashin ganin al’adarsu duk wata.
"Wasu matan na iya kaiwa wata uku, wasu ma har wata shida, kafin su ga jinin al’adarsu ko kuma zai fara zuwa yana raguwa da kaɗan-kadan har ya ɗauke.
"Idan ka tambayi masu wannan matsalar, za su ce maka gashi na fito musu a fuska. Sannan in ka duba jikinsu za ka ga suna da gashi kamar a cikinsu irin yadda na maza ke girma.
"Sannan idan aka yi musu hoto (scanning) za a ga akwai ƙwayaye da yawa a cikin wannan gidan ƙwan waɗanda ba su gama nuna ba. Waɗannan na cikin alamomin wannan larurar da za a iya gani."
Game da yadda ake gano cutar, Dr Sadiya ta ce:
"Akan yi gwajin wannan sinadarin na Testosterone idan mace ta zo da gashi a fuska. Idan ya yi ƙasa da 200, to an san cewa ba cutar daji take ɗauke da ita ba. Idan ya yi sama da haka za a fara tunanin ƙila kansa ce.
"Akwai kuma wasu gwaje-gwaje da za a yi don gano cutar POS. Ana iya yin wasu ƙarin gwaje-gwaje don gane ainahinmatsalar."
Illolin cutar POS
Mata marasa aure
Ga macen da ba ta yi aure ba, al’adarta za ta dinga yi mata wasa - wato ba za ta dinga ganin jinin haila duk wata ba, ko kuma ya dinga zuwa mata kaɗan kaɗan, in ji Dr Sadiya.
"Wasu lokutan ma in aka tamabayi macen za ta ce ya ɗauke kwatakwata ba ta gan shi ba tun wata uku da suka wuce."
Mata masu aure
"Ga matan da suke da aure kuma suke da niyyar samun ciki, za a ga wani lokaci suna fuskantar jinkiri, saboda haka dole sai an ba su magunguna kafin su samu cikin."
Ko larurar na da magani?
Ita ma amsar wannan tambayar ta danganta ne kan abin da ya haifar da matsalar.
Dr Sadiya ta ce: “Idan babu abin da ya kawo ta, wani lokacin ana ba su shawarar su dinga cire gashin. In kuma an san abin da ya kawo shi, za a iya ba da magani da zai sa shi ya ragu, ko kuma a yi maganin abin da ya kawo shi."










