An ci Chelsea duk da ƴan wasa 11 da ta ɗauka kan fara kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta je ta doke Chelsea 2-0 a wasan makon farko a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Stamford Bridge.
Shi ne karon farko da sabon koci, Enzo Maresca ya ja ragamar Chelsea, wadda ta ɗauko daga Leicester City a kakar da ta wuce.
Chelsea, wadda ta yi ta shida a bara ta raba gari da koci, Mauricio Pochettino, sannan ta maye gurbinsa da Marresca.
Minti na 18 da take leda ne City ta fara cin kwallo ta hannun Erling Halland - na 106 kenan da yake da hannu a wasa na 100 a kungiyar Etihad, wanda ya ci 91, sannan ya bayar da 15 aka zura a raga.
Tun daga kakar 2022-23, Erling Haaland ya ci ƙwallaye da yawa a Premier League cikin watan Agusta sau 13 fiye da yawan na Chelsea 11 da Manchester United guda tara.
Daga baya ne City ta kara na biyu ta hannun Mateo Kovacic, saura minti shida a tashi daga fafatawar ta hamayya.
Ba a fara karawar ba da Raheem Sterling na Chelsea karon farko da buɗe wasan da ba a fara Premier League da shi ba tun 2012/13, wanda ya yi kaka 11 kenan a jere.
Chelsea ta kashe £185m wajen sayen ƴan wasa 11 a bana, kenan Maresca yana da manyan ƴan ƙwallo sama da 40 a ƙungiyar.
Da wannan sakamakon City ta yi wasa 24 a jere a Premier League ba tare da rashin nasara ba, tun bayan da Aston Villa ta doke ta 1-0 a cikin watan Disamba.
Wannan shi ne karo na takwas a jere da City ta fara wasan farko a Premier League a waje.
City ta lashe wasa na 13 daga 14 a farkon fara Premier League, idan ka cire wanda Tottenham ta doke ta 1-0 a 2021-22.
Kenan Chelsea ba ta yi nasara ba a karo na 10 da ta fuskanci City a dukkan fafatawa, tun bayan 1-0 da ta ci a Champions League a 2021, wadda ta yi canjaras biyu aka doke ta takwas daga ciki.
Manchester City ta ci wasa na huɗu da canjaras a fafatawa biyar baya da ta je ta fafata a Stamford Bridge.
Ƴan wasan da suka buga wa Chelsea da Manchester City karawar

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan wasan Chelsea 11: Sanchez; Gusto, W Fofana, Colwill, Cucurella; Lavia, Caicedo, Fernandez; Palmer, Jackson, Nkunku.
Masu jiran ko-ta-kwana: Jorgensen; Badiashile, Tosin, Veiga; Dewsbury-Hall, Madueke, Mudryk, Neto, Guiu.
Savinho ya fara buga wa Manchester City tamaula bayan jinya.
Ƴan wasan Man City 11:Ederson; Lewis, Akanji, Dias, Gvardiol; Kovacic, De Bruyne; Savinho, Silva, Doku; Haaland
Masu jiran ko-ta-kwana: Ortega, Walker, Stones, Ake, Grealish, Nunes, Foden, O'Reilly, McAtee










