Amurka ta cimma yarjejeniyar albarkatun kasa da Ukraine

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ma'aikatar Baitul Malin Amurka ta sanar da cimma yarjejeniya da Ukraine kan hadin-gwiwa wajen tafiyar da harkokin albarkatun kasarta da makamashi.

Kasashen biyu sun yarda da kafa wani asusun zuba jari na sake gina Ukraine da farfaɗo da tattalin arzikita.

Sakataren baitul malin ƙasar Amurka, Scott Bessent ne ya sanar da rattaba hannu a wannan yarjejeniya a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya na mai cewa; "Godiya da jinjini ga shugaba Trump bisa nuna jajircewa wajen abbatuwar zaman lafiya mai dorewa, ina farin cikin sanar da cewa a yanzu an rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin-gwiwa irinta ta farko a tarihi da za ta inganta tattalin arziki tsakanin Amurka da Ukraine, zamu kafa Hukumar Amurka ta sake gina Ukraine.

"Wannan hadin-guiwa za ta bamu damar aiki kafada da kafada da Ukraine wajen Inganta tattalin arziki, kadarori da raya birnin da kadarori.

"Wannan na sake nuna jajircewar Trump wajen ganin cigaban kasar Ukraine da kawo karshen yakinta da Rasha.

Firaministan Ukraine, Denys Shmyhal, ya ce kowanne bangare zai kasance yana da kashi 50 cikin 100 na 'yanci tafiyar da kudaden hukumar, sannan ribar da aka samu za a sake juyasu a cikin Ukraine.

Shugaban kwamitin harkokin wajen Ukraine, Oleksandr Merezhko, wanda alhakin bai wa majalisar kasar shawarar kada kuri'ar amincewa da wannan yarjejeniya ya rataya a wuyansa, ya ce tabbas wannan tsari ne da kasashen biyu za su ci moriya.

"A karkashin wannan tsari ina iya cewa kowanne bangare ya yi nasara, Amurka da Ukraine kowanne ya samu abin da yake so, dama da farko mun yi kokarin kaucewa yanayi da zamu iya fadawa ko cutuwa ta fuskar barzanar soji wanda wannan taimako a yanzu zai samu, babu batun ya zame mana bashi.

"Da wannan tsari da kuma abubuwan da ke kunshe a yarjejeniya ina iya cewa zance na gaskiya babu wani abin cutarwa, kuma hakan ba zai kangemu ko dakushe muradinmu na zama mamba tarayyar Turai ba.

Ana dai ganin za a kwashe tsawon shekaru kafin a cimma ribar wannan yarjejeniya, sannan dole sai majalisar Ukraine tayi zama domin amincewa da sharudan yarjejeniyar.

Amma dai tabbas yarjejeniya ce da za ta kwantar da hankula a Ukarine, sannan ta kasance babban koma baya ga Rasha.

A makon da ya gabata shugaba Trump ya ce yana ganin a shirye takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky yake ya amince ya sallama yankin Crimea ga Rasha don cimma zaman lafiya.

A baya shugaban na Ukraine ya sha nanata cewa ba zai sallama yankin da Rashar ta kwace a 2011 ba.

Kazalika shugaba TrumP ya kuma roki Shugaba Putin na Rasha ya dakatar da bude wuta ya dawo teburin sulhu da kulla yarjejeniya, wani abu da ya ce ana iya cimmawa cikin makwanni biyu.

Trump ya yi wadannan kalamai ne a lokacin ganawa da manema labarai bayan ya koma Amurka daga Vatican, inda ya yi wata 'yar ganawa da takwaran nasa na Ukraine, Shugaba Zelensky kafin jana'izar Fafaroma Francis.

Ita dai Ukraine ba sau daya ba ba kuma sau biyu ba ta sha nanata kin yardarta tare da yin watsi da maganar sallama wani yankin kasarta ga Rasha, tana mai jaddada cewa duk wani batu da ya shafi kasa za a tattauna shi ne kawai bayan an amince da dakatar da bude wuta.

A shekara ta 2022 ne Rasha ta kaddamar da cikakken yakin mamayar Ukraine kuma a yanzu haka tana rike da kusan kashi 20 cikin dari na kasar ta Ukraine.