Me ya bambanta farashin man fetur a Najeriya da wasu ƙasashen Afrika?

ghh

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ba kowace ƙasa ce a nahiyar Afirka ke da arzikin man fetur ba. Wasu ƙasashen na dogaro ne da shigo da tataccen man fetur daga wasu ƙasashe, yayin da wasu, duk da cewa suna da ɗanyen mai mai yawa, ba su da isassun matatun mai da za su iya biyan buƙatarsu ta cikin gida.

Ƙasashe irinsu Najeriya, Afrika ta Kudu, Libya da Sudan na da arziƙin man fetur, duk da yake wasu ƙasashen na fama da ƙalubale.

Kasancewar ƙasa na da arzikin man fetur ba shi ke nuna lallai ƴan ƙasar za su samu farashi mai sauƙi ba.

Duk da cewa ana sayar da ɗanyen mai a kasuwar duniya da dala, farashin man fetur da ake sayarwa ga jama'a ya bambanta sosai daga wata ƙasa zuwa wata. Wannan na da alaƙa da abubuwa da dama, ciki har da tallafin gwamnati, haraji, ƙarfin kuɗin ƙasa, kuɗin shigo da mai da kuma yadda ake samar da shi a cikin gida.

A halin yanzu, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya kai sama da dala 100 kan kowace ganga, saboda rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya.

Da zarar farashin man fetur ya tashi kusan komai a wasu ƙasashen na sauyawa, kama daga sufuri, kayan masarufi da sauransu. Amma ba duka ƙasashen ke barin farashin ya yi tasiri ba saboda wasu gwamnatoci na bayar da tallafin domin rage raɗaɗin da hauhawar farashin ke jefa jama'a.

BBC ta yi nazari kan bambancin farashin man fetur a wasu ƙasashen nahiyar da kuma yadda yake a Najeriya.

Farashin man fetur a wasu ƙasashen

Najeriya - Ƙasa ce da ke da tarin arzikin man fetur da ake haƙowa a Kudancin ƙasar. Sai dai rashin matatun da ke aiki a cikin gida ya sa ƙasar ba ta iya tace shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farashin man fetur a ƙasar ya kai kusan naira 1,500 wato dala $1 a canjin kuɗin ƙasar. Tsadar na zuwa ne bayan da matatar man Dangote ta kara farashin man fetur, kuma gwamnatin ƙasar ba ta biyan tallafi.

Ƙasar ta cire tallafin man fetur a 2023, lamarin da ya sa farashin man fetur ya tashi sosai, kuma hakan ya shafi sufuri da shafar kusan kowane fanni da jefa da dama na ƴan ƙasar cikin matsin tattalin arziki.

Nijar - Kamar yadda bayanan Global Petrol Prices suka nuna, Nijar ƙasa ce da ke da arzikin man fetur da take haƙowa a yankin Agadem tun shekarar 2011. A halin yanzu, farashin man fetur a ƙasar yana nan a kan Sefa 499 (kusan dala $0.85 ko naira ₦1,127).

Kamaru - Kamaru tana haƙo danyen mai a tekunta, amma matatar mai guda ɗaya tilo da take da ita ta samu matsalar gobara, wanda hakan ya sa ƙasar ta dogara kacokan kan shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje. Farashin mai a ƙasar ya tashi sosai inda ya kai 840 XAF (kusan dala $1.49 ko naira ₦1,975 a kowace lita) sakamakon janye tallafin mai da gwamnati ta yi.

Chadi - Chadi tana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka masu arzikin mai kuma tana da matatar mai ta Djarmaya wadda ke tace mata man da take amfani da shi. A yanzu haka litar fetur na tsakanin 518 XAF (kusan dala $0.85 ko ₦1,127).

Afirka ta Kudu - Afirka ta Kudu ba ta da wani arzikin danyen mai na azo-a-gani a ƙasarta, kuma yawancin tsoffin matatun mai na ƙasar sun daina aiki, wanda ya sa ta dogara gaba ɗaya kan shigo da tataccen mai daga ketare.

Farashin mai ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai Rand 26.92 (kusan $1.67 ko naira ₦2,214 a lita ɗaya) na kudin ƙasar.

Ghana - Tana haƙo danyen mai a rijiyoyin Jubilee da ke cikin teku, kuma ko da yake tana da matatar mai ta Tema (TOR), matatar ba ta cika aiki yadda ya kamata ba, wanda ya sa ƙasar ke shigo da mafi yawan tataccen mai daga waje. A halin yanzu, farashin mai a Ghana ya kai Cedis ¢16.77 (kusan dala $1.26 ko naira ₦1,671).

Benin - Benin ba ta da arzikin man fetur. A halin yanzu, farashin mai a ƙasar ya kai 725 XAF (kusan dala $1.28 ko naira ₦1,697) bayan da gwamnatin ƙasar ta ƙara farashin don daidaitawa da kasuwar duniya.

Kenya - Ita ma Kenya ba ta da arzikin man fetur. Hukumar EPRA ta ƙasar ce ke kayyade farashin, inda a yanzu haka litar fetur ke kan Shiling 214.03 (kusan $1.65 ko ₦2,188).

Sudan - Tana da arzikin man fetur kuma tana da matatun mai a cikin gida. Farashin mai a ƙasar ya kai dinar 630 SDG (kusan $0.70 ko ₦928).

Senegal - Tana cikin ƙasashen da ke hako danyen mai da iskar gas a cikin teku. A yanzu haka, farashin fetur a kasar ya tashi kai Sefa 990, wanda yake daidai da kusan $1.75 ko kuma naira ₦2,320 kan kowace lita ɗaya.

Bambancin farashin a naira

Ga yadda farashin yake a tsakanin ƙasashen a kuɗin ƙasar da dala da kuma Naira

Farashin man fetur a tsakanin ƙasashen Afrika
Bayanan hoto, An haɗa hoton da ƙirƙirarriyar basira daga bayanan da aka tattara daga Global Petrol Prices

Ƙasashen Afrika da suka fi sauƙi da tsadar man fetur

  • Libya

Libya ita ce ƙasa ta farko a Afirka wajen yawan arzikin man fetur, kuma tana da matatun mai ko da yake rigingimun a ƙasar na shafar su. Saboda tsananin tallafi da gwamnati ke ba da wa, Libya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa sauƙin mai a Afirka (kuma ta biyu a duniya), inda litar fetur ke Dinar 0.15 LYD kacal (wato dala $0.024 ko naira ₦32).

  • Malawi

A halin yanzu, Malawi ce ke da mafi tsadar fetur a Afirka, bisa bayanan farashin fetur na 7 ga Satumba 2026 daga Global Petrol Prices. Farashin ya kai kusan dala $3.24 kan kowace lita, in ji Global Petrol Prices.