Abin da malaman jami'a suka faɗa wa masu neman su goyi bayan Tinubu

..

Asalin hoton, Presidency/Nig

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wata ja-in-jar siyasa ta kaure tsakanin malaman manyan makarantu a Najeriya, bayan matakin da wasu daga cikin Lakcarori suka ɗauka na bayyana goyon bayansu ga shugaba Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.

Ganawa da malaman jami'o'in ta haifar da ce-ce-ku-ce a fadin ƙasar, inda aka ruwaito cewa sun yi mubaya'ar ne da sunan Lakcarori a arewacin Najeriya.

Tuni wasu Lakcarori a ƙasar suka bayyana cewa ba da yawunsu aka ayyana goyon bayan ba.

Sai dai daga cikin malaman da suka karɓi goron gayyatar, sun ce taron ba yana nufin goyon bayan wata manufar siyasa ba ne, face tattauna manufofin gwamnatin Tinubu da inda ta samu kurakurai domin a gyara.

Sai dai an ce wadanda za su goyi bayansu sun lissafa sharudda da idan aka cika musu za su goyi bayansu.

Me ya faru a taron?

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari ne ya shirya taron a ƙarshen mako.

Wasu daga cikin malaman jami'oin sun ƙi amsa gayyatar saboda sun ce hakan ya saɓa da tsarin aikinsu na gwamnati.

"An tura min da wasiƙa cewa ana so ne mu zo a tattauna a faɗi abubuwan da gwamnati ta yi ba daidai ba," in ji Dr Hashim Sulaiman, malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

A wajen taron dai an buƙaci malaman su yi wa Tinubu mubaya'a domin ya zarce.

Sai dai Dr Mukhtar Elkasim daga jami'ar ta ABU da shi ma ya halarci taron ya ce su malaman jami'a na da ruwa da tsaki a kan kowane lamari, kuma a wajen taron an bayyana abubuwan da gwamnati ta yi ne.

Ya ce sun kuma faɗa wa gwamnati halin da ƙasar ke ciki da kuma matsin tattalin arziki da ma inda ya kamata ta gyara.

"Gwamnati an ja mata hankali game da kura-kuran da take da shi, ana cikin mawuyacin hali," in ji shi.

'Abin da ya sa ba mu je ba'

Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar Dr Hashim Sulaiman, gayyatar da aka miƙa musu ƙarara tana buƙatar su ayyana goyon bayansu ga Tinubu, wanda a ganinsa ya saɓa da aƙidarsa da yanayin aikinsa.

Ya ce idan ya yi hakan yana ganin bai tsaya a tsakiya ba saboda muhimmin abin da ya kamata ya maida hankali a kai shi ne koyarwa da bincike.

"Abin da ake so idan mun gama [taron] shi ne, mu nuna goyon bayanmu ga shugaba mai ci yanzu, domin ya zarce," in ji shi.

"Aiki na na malamin jami'a shi ne bincike da koyarwa..., ba shi daga cikin aiki na a matsayina na malamin jami'a in je in ce na goyi bayan wani ɗan siyasa".

Malamin ya ce labaran da aka yaɗa cewa "Lakcarorin arewacin Najeriya sun goyin bayan Tinubu" ba gaskiya ba ne saboda adadin mutanen da suka je taron ma ba su wakiltar wani kashi mai ƙarfi na malaman.

"In da a wasiƙar sun ce za mu tattauna ne mu faɗi inda aka yi daida, da inda ba a yi daidai ba, to da zan je".

Ya ce idan har malaman jami'o'i suka tsunduma cikin siyasa mutane za su daina ɗaukar ra'ayinsu da muhimmanci domin karkata tunaninsu zuwa ga wata siyasa.

Dr Hashim ya ƙara da cewa an sha gayyatar shi a taruka na gwamnati, amma kuma ba wai don su nuna goyon bayansu ba.

Abin da malaman suka faɗa wa gwamnati

Dr Mukhtar Elkasim duk waɗanda suka je taron a matsayin raɗin kanshi ya je ba da sunan ƙungiya ba da har za a ayyana cewa sun nuna goyon bayansu, saboda kowane ɗanƙasa na da damar ya bayyana ƙungiyar da yake goyon baya.

Ya kuma ce babu inda aka ce sai sun goyi bayan ɗan siyasa ko kuma zuwansu taron ya nuna tilas.

A ganinsa bai kamata malaman su ware kansu gefe suna sukar gwamnati ba tare da sun je sun ji abin da gwamnati ke yi ba, inda ya ce wannan babbar dama ce da za su fahimci gwamnati.

"Ko a wajen taron sun ce, bai kamata a ce malaman jami'o'i sun ƙi shigowa cikin harkokin siyasa ba," in ji shi saboda yadda suka nuna inda aka yi ba daidai ba ko kuma koyar da al'umma.

Sai dai Dr Elkasim ya ce duk da haka sai da suka ja hankalin gwamnati da faɗa mata gaskiya ɓaro-ɓaro kan halin da ake ciki na rashin tsaro da matsin tattalin arziki.

Ya kuma ƙara da cewa sun faɗa wa gwamnatin inda take da kura-kurai da inda za ta gyara, ba wai kawai kai tsaye suka nuna mata goyon baya ba.

Bugu da ƙari ba a matsayin ƙungiya suka je taron, kamar yadda aka ruwaito labaran a baibai.