Man City ta fara wasan sada zumunta da rashin nasara a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta fara da rashin nasara a wasannin atisayen tunkarar kakar 20224/25, bayan da Celtic ta doke ta 4-3 a Amurka.
Shi ne wasan farko da ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta yi a shirin da take na kare Premier League da ta lashe a bara na hudu a jere.
Waɗanda suka ci wa City ƙwallo sun hada da Oscar da Maximo Perrone da kuma Erling Haaland, wanda ya lashe takalmin zinare a yawan cin ƙwallaye karo biyu a jere a Ingila.
Celtic kuwa ta ci kwallo ta hannun Kyogo Furuhasi da Luis Palma da kuma Nicolas-Gerrit Kuhn da ya zura biyu a raga a fafatawar.
City za ta buga wani wasan sada zumunta ranar 27 ga watan Yuli, inda za ta fuskanci AC Milan a birnin New York a Amurka.
Daga nan ne ƙungiyar Etihad za ta kara da Barcelona a Orlando ranar 30 ga watan Yuli, sannan ta karkare da fuskantar Chelsea a Columbus ranar 3 ga watan Agusta.
Ita kuwa Celtic ta kusan kammala wasannin atisayen tunkarar kakar bana, bayan da za a fara babbar gasar tamaula ta Scotland ranar 3 ga watan Agusta.
Ranar 27 ga watan Yuli, Celtic za ta buga wasan sada zumunta na karshe a Amurka, inda za ta fafata da Chelse, bayan da ta yi nasara kan DC United 4-0 da doke City 4-3.
Ranar 10 ga watan Agusta za a buga Community Shield tsakanin Manchester United da Manchester City a Wembley.
A cikin watan Mayu ƙungiyoyin Manchester sun kara a wasan karshe a FA Cup a Wembley, inda United ta yi nasarar lashe kofin.
Ana buga Community Shield tsakanin wadda ta lashe FA Cup a bara da wadda ta ɗauki Premier League, domin buɗe labulen fara babbar gasar tamaula ta Ingila.












