Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Havertz ya yi sanadin da Chelsea ta samu maki uku a kan Palace
Kungiyar Chelsea ta yi nasarar cin Crystal Palace 1-0 a wasan mako na 20 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.
Kungiyoyin sun tashi ba ci a minti 45 din farko daga nan suka je hutu a karawar da suka yi a Stamford Bridge.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Kai Havertz ya ci wa Chelsea kwallo a minti na 64, bayan da Hakim Ziyech ya bugo masa tamaular.
Wannan sakamakon da Chelsea ta samu zai dan rage matsi ga koci Graham Potter, wanda baya samun sakamakon da kungiyar ke bukata.
Chelsea ta sha kashi a wasa uku a jere a dukkan fafatawa har da wanda Manchester City ta fitar da ita daga FA Cup na bana.
Dan kasar Jamus, mai shekara 22 ya kusan kara na biyu a raga a wata kwallon da Mason Mount ya buga masa, amma ta yi fadi ta fita waje.
Palace ta kusan farke kwallon, bayan da Cheick Doucoure ya buga kwallo daga nesa ya nufi raga, sai dai Kepa Arrizabalaga ya sa hannu ya yi waje.
Chelsea ta ci gaba da zama a matakinta na 10 a kan teburin Premier League da maki iri daya da na Liverpool wadda take ta taran teburi.
Ita kuwa Palace tana ta 12, kuma wasa na biyar da ta sha kashi daga shidan da ta fafata a dukkan karawa.