AC Milan ta dauki Divock Origi

Asalin hoton, Rex Features
An wallafa
AC Milan ta dauki Divock Origi, wanda kwantiraginsa ya kare a Liverpool, bayan kammala kakar Premier League da ta wuce.
Yarjejeniyar dan wasan tawagar Belgium, mai shekara 27 ta kare a Anfield, ya kuma sa hannu kan kwantiragin kaka hudu a San Siro.
Origi ya ci kwallaye masu mahimmaci a Liverpool, har da ta biyu da ya ci Tottenham a wasan karshe a Champions League da kungiyar Anfield ta yi nasara da ci 2-0 a 2019.
Ya koma taka leda a Liverpool a 2014 da cin kwallo 41 a wasa 175 da ya yi mata.
AC Milan ta lashe Serie A a kakar da aka kammala a karon farko tun bayan shekara 11, rabon da ta dauki kofin babbar gasar Italiya.







