Origi yana Italiya domin auna koshin lafiyarsa kan komawa AC Milan

An wallafa

Tsohon dan kwallon Liverpool, Divock Origi ya je Italiya, domin auna koshin lafiyarsa a shirin da yake na komawa AC Milan da taka leda.

Dan wasa Origi ya bar Liverpool, bayan da kwantiraginsa ya kare a karshen watan Yuni, bayan kammala gasar Premier League.

Mai shekara 27 ya ci kwallo mai mahimmaci a wasan da Liverpool ta doke Tottenham 2-0 ta lashe Champions League a 2019.

Dan wasan tawagar Belgium ya koma Anfield a 2014, ya kuma ci kwallo 41 a fafatawa 175 da ya yi mata.

AC Milan ce ta lashe Serie A, kakar da ta wuce a karon farko tun bayan shekara 11, abokiyar hamayyarta Inter Milan ita ce ta yi ta biyu.