Fernandinho ya koma Athletico Paranaense

An wallafa

Athletico Paranaense ta sake daukar Fernandinho, kungiyar da ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa.

Tsohon kyaftin din Manchester City ya koma kungiyar Brazil, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar 2021/22.

Mai shekara 37, tsohon dan kwallon tawagar Brazil ya fada cewar ''Kungiyoyi da yawa sun yi zawarci na, amma na zabi tsohuwar kungiyata, domin na saka mata da abin da ta yi min.''

Fernandinho ya bar Etihad, bayan kaka tara da ya yi a City.

Wanda ya lashe kofin Premier League biyar, ya koma Athletico, bayan barin kungiyar shekara 17 zuwa Shakhtar Donetsk.

Tsohon kociyan Chelsea, Luiz Felipe Scolari shi ne yake horar da Athletico.