Ko Liverpool za ta ci Crystal Palace a wasanta na biyu a Premier League?

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasa na biyu a gasar Premier League da za su kara a Anfield ranar Litinin.
Liverpool tana da maki daya, bayan da ta tashi 2-2 a wasan farko a gidan Fulham a makon jiya, wadda ta fara buga Premier a kakar nan.
Palace kuma bata da maki ko daya, bayan da Arsenal ta doke ta 2-0 a wasan makon farko a Selhust Park karawar hamayya.
Kungiyar da Patrick Vieira ke jan ragama ta yi rashin nasara a wasa 10 a jere a hannun Liverpool.
Sai dai koci Jurgen Klopp ya fara shan kashi a matakinsa na mai jan ragamar Liverpool da ci 2-1 a hannun Palace cikin watan Nuwambar 2015.
Liverpool za ta buga karawar ba tare da Thiago Alcantara ba, wanda ya ji rauni a wasa da Fulham a makon jiya, zai yi jinyar wata daya.
Har yanzu Curtis Jones da Alex Oxlade-Chamberlain na jinya, sai dai Naby Keita ya samu sauki daga rashin lafiya da ya yi.
Kawo yanzu Crystal Palace za ta buga wasan ba tare da James McArthur da kuma James Tomkins ba.
Watakila Michael Olise ya yi wa Vieira karawar, wanda ya yi atisaye bayan da ya sha jinya.
Mohamed Salah ya ci kwallo 119 a Premier League a Liverpool, Steven Gerrard ne gabansa mai 120 da kuma Robbie Fowler mai 128 a tarihin kungiyar.
Cikin wasa biyar da Palace ta buga a bara a Premier League ranar Litinin ta ci karawa daya da canjaras hudu, kenan ba a doke ta ba.











