Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Real Madrid da suka je Man City buga Champions League
Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a zagayen quarter final a Champions League ranar Laraba a Etihad.
Kungiyoyin sun tashi 3-3 a wasan farko da suka buga a makon jiya a Spain, inda Bernardo Silva da Manuel Akanji da Josko Gvardiol suka ci wa City kwallayen.
Ita kwa Real Madrid, Ruben Dias ne ya fara cin gida, sai Rodrygo ya zura na biyu a raga da kuma Federico Valverde ya ci na uku a wasan na hamayya.
Kaka uku kenan a jere ana haduwa tsakanin kungiyoyin a Champions League, inda a 2021/22, Real Madrid ta kai zagayen gaba da cin 6-5 gida da waje,
Sai dai a bara City ce ta kai bante da cin 5-1, bayan da suka tashi 1-1 a Spainiya, sannan aka ci Real 4-0 a Etihad.
Kungiyar da Pep Guardioa ke jan ragama ba a doke ta ba a dukkan karawa a gida tun daga Nuwambar 2022, kenan tun bayan da Brentford ta ci 2-1 a Etihad a Premier League.
Haka kuma City ta yi nasara uku baya a kan Real Madrid a gida da cin kwallo 10 aka zura mata uku a raga.
Wannan shi ne wasa na 12 da za a kece raini tsakanin kungiyoyin, inda City ta yi nasara hudu da canjaras hudu, Real ta ci karawa uku.
Kungiyar Etihad za ta samu kwarin gwiwar buga karawar, bayan da mai tsaron baya Kyle Walker ya murmure, wanda ya ji rauni a wasan Ingila a watan jiya.
Ana sa ran Kevin de Bruyne zai buga fafatawar, wanda bai samu yin na farko ba a Spaniya, bayan da tun farko an sanar da shi cikin wadanda za su kara a Santiago Bernabeu.
Nathan Ake bai je Spaniya ba a wasan farko, amma ya buga fafatawar da City ta dura 5-1 a ragar Luton Town ranar Asabar a gasar Premier League.
Wadanda ke jinya a Real Madrid sun hada da Thibaut Courtois da David Alaba, yayin da Aurelien Tchouameni ke hukuncin dakatarwa wasa daya, bayan katin gargadi uku da aka yi masa a gasar zakarun Turai.
Real Madrid tana da Champions League 14 jimilla, yayin da City take da daya a karon farko a tarihi da ta dauka a bara.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa y Fran.
Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger y Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos y Arda Güler.
Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu y Brahim.
Manchester City na fatan maimaita lashe kofi uku a bana kamar yadda ta yi a bara.
City ta lashe Premier League da FA Cup da Champions League, wadda a bana tana ta daya a kan teburi da maki 72 da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal da Liverpool a Premier League.
Haka kuma za ta buga daf da karshe a FA Cup da Chelsea, sannan tana fatan kai wa daf da karshe a Champions League idan ta gama wasa da Real Madrid.