Man United ta je ta ci Fulham da kyar da gumin goshi

Asalin hoton, Getty Images
Fulham ta yi rashin nasara a gida a hannun Manchester United da ci 1-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League ranar Asabar.
Daf da za su tashi wasan ne kyafti, Bruno Fernandes ya ci kwallon da ya bai wa United damar hada maki uku.
Kenan United tana da maki 18, bayan karawa 11 da cin fafatawa shida aka doke ta biyar ba tare da canjaras ko daya ba.
Ko a bara United doke Fulham gida da waje ta yi a gasar Premier League da kuma kunnen doki da suka tashi a FA Cup, inda United ta kai zagayen gaba.
Kuma wasa uku kacal Fulham ta yi nasara daga 33 kenan da ta fuskanci kungiyar Old Trafford.
Rabon da Fulham ta yi nasara a kan United a wasa 16 a babbar gasar tamaula ta Ingila tun Disambar 2009,, wadda ta yi canjaras uku aka doke ta karo 13.
Ranar Laraba United za ta ziyarci FC Copenhagen, domin buga wasa na hur-hudu a rukunin farko a Champions League.
Ranar 2 ga watan Oktoba, United ta yi nasara 1-0 a kan Copenhagen a Old Trafford a gasar ta zakarun Turai.
Ranar 12 ga watan Nuwamba, Fulham za ta ziyarci Aston Villa, domin karawa a wasan mako na 12 a Premier League a Villa Park.












