Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United na shirin ɗaukar daraktan wasannin Newcastle
Manchester United ta yi wa daraktan wasannin Newcastle Dan Ashworth tayin komawa ƙungiyar.
Ashworth ya jima yana da kyakkyawar alaƙa da shugaban wasannin Ineos, Sir Dave Brailsford.
Ba dai a fara tattaunawa ba kan yadda za a biya kudaden da ya kamata na barin daraktan daga Newcastle tsakanin ƙungiyoyin biyu ba ya zuwa yanzu.
Idan har wannan yarjejeniya aka cimma ta, hakan zai sake zama wata gagarumar nasara ga Inoes, wanda ake neman tabbatar masa da kashi 25 cikin 100 na Manchester United a farkon makon gobe.
An fahimci cewa shi kan shi Ashworth ya matsu ya koma Old Trafford, tun bayan ƙawancen da ke tsakaninsa da Brailsford lokacin da yake da muƙami a hukumar FA.
Har yanzu Ashworth na da sauran lokaci da ya rage masa, kamar yadda ya faru a lokacin da yake shirin barin Brighton zuwa Newcastle a 2022.
Mai shekara 52 na da tarihin zama shahararren daraktan wasanni kuma ana cewa shi ne sirrin nasarar da matasan Ingila suka samu a 2017, lokacin da suka yi nasarar lashe kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 17 da 20.
Kuma ya taimaka wajen daga darajar Brighton a Premeir wajen da kuma yadda ta nada Graham Potter a matsayin kocinta bayan ta kori Chris Hughton
Idan har cinikin ya faɗa, da yiwuwar Ashworth zai iya samun cikakken iko a United.
Manchester United ba ta ƙoƙari kan yadda take sayan 'yan wasanta a shekarun nan, yayin da tsohon shugaban ƙungiyar Richard Arnold candidly ya amsa cewa sun kashe fan biliyan 1 kuma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Ya kafa misali da ɗan wasan Brazil Antony mai shekara 23, wanda shi ne mutum na biyu mafi tsada a ƙungiyar bayan Paul Pogba, wanda hakan ke nuna cinikin da ake yi ƙarƙashin Erik Ten Hag ba a samun yadda ake so.