Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya a Jihar Rivers: Jiha mai arzikin man fetur maras lantarki
Akwai ƙara iri-iri cikin wannan shagon ɗinki da ke tsakiyar jihar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Najeriya.
Ƙarar kekunan ɗinki guda huɗu da na yankan almakashi da kuma ƙarar dutsen gugar da ake yi kan tufafin da aka yayyafa wa ruwa.
Ana jin ƙarar injin janareton da suke amfani da shi. Yana can ɓoye a bayan shagon nasu, to sai dai ƙararsa da hayaƙinsu ba su ɓoyu ba.
''Ina da injin janareto guda biyu, ko da ɗaya zai lalace'', in ji Ozu Adah wanda shi ne mai gudanar da wannan shago a garin Choba da ke kusa da jami'ar jihar Rivers.
Kamar sauran miliyoyin masu ƙananan sana'o'i a Najeriya, telan mai shekara 37 bai dogara da wutar lantarkin ƙasar ba, wadda ba ta wadatar da ƙasar.
Mafi yawan al'umar ƙasar waɗanda aka kiyasta yawansu ya kai miliyan 210 kan samar wa kansu wutar lantarkin da suke buƙata.
Najeriya - wadda ake kallo a matsayin wadda ta fi kowacce ƙasa ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka - na amfani da injinan janareta daban-daban waɗanda aka ƙera a ƙasashen China da Lebanon.
''Tun da aka haifeni ban taɓa ganin wutar lantarki ta daidaita a ƙasar nan ba. Muna kiran kanmu a matsayin giwar Afirka, to amma ba mu da tsayayyiyar wutar lantarki,'' in ji Mista Adah.
Duk da cewa Allah ya albarkaci ƙasar da ɗimbin arzikin man fetur da albarkatun iskar gas, da ruwa da hasken rana, gwamnatocin da suka jagorancin ƙasar tun bayan samun 'yancin kai sun kasa wadata ƙasar da wutar lantarki.
A yayin da ya rage 'yan makonni a gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa, duka manyan 'yan takarar shugabancin ƙasar uku waɗanda suka haɗar da Bola Ahmed Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na LP, sun bayyana samar da wutar lantarki a cikin manyan manufofinsu na yaƙin neman zaɓe.
Mista Adah na kashe aƙalla naira 3,000 a kowacce rana wajen sayen man fetur domin zuba wa injinsa don gudanar da aiki a kullum.
To sai tun watan Nuwamban bara, ƙasar na fuskantar ƙarancin man fetur, wadda a baya-bayan nan ta ƙara munana, lamarin da yake tilasta wa mutanen ƙasar da dama kwana a kan layin gidajen mai.
Abin na fusata shi idan ya tuna cewa yana zaune ne a jihar da tafi kowacce jiha arzikin man fetur a Najeriya.
A lokacin da yake yaro burinsa shi ne ya yi aiki a ma'aikatar ɗanyen mai kamar yadda mahaifinsa ya yi. To amma a lokacin da ya kammala jami'a bai samu aiki a ma'aikatar ba.
A maimakon haka sai ya rungumi sana'ar ɗinki, wadda tun yana yaro mahaifiyarsa ke yi.
'Ba a samun kuɗi a sana'o'in da ke amfani da lantarki'
Mutanen da ke aiki da lantarki a sana'o'insu na ƙorafin cewa sana'o'in nasu ba sa bunƙasa, saboda rashin samun riba sakamakon rashin wadutuwar wutar lantarkin.
Najeriya na da arzikin cubic tiriliyan 200 na albarkatun iskar gas, ta fi kowacce ƙasa arzikin a Afirka sannan kuma ita ce ta tara a duniya.
To sai dai masu zuba jari na korafin cewa tsauraran dokoki da gwamnati ta sanya na karya musu gwiwa.
"Babu mutumin da zai zuba jari bayan da tabbata ƙarara a gare shi cewa faduwa zai yi'' in ji Olumuyiwa Abiodun, shugaban kamfanin Eden Power, wani kamfani mai zaman kansa da ke samar da lantarki.
Mutane da dama da ke amfani da lantarki kamar Mista Adah tare da dubban gidajen da ke amfani da lantarkin a garin Choba, ba su da mita, dOn haka dole su biya bil din da gwamnati take sanya musu a wata.
Mista Adah na biyan 8,000 a duk wata a matsayin bil ɗin lantarkin a gidansa da shagon nasa wanda ke da aƙalla ɗakuna takwas.
Da yawa daga cikin 'yan Najeriya ba sa biyan kudin wuta
Jiha ce mai matuƙar muhammanci a zaɓe
Jihar na da masu rajistar zaɓe miliyan 3.5, abin da ya sanya ta zama jiha ta hudu da ke da yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, to sai dai da alama ƙuri'un jihar za su karkasu zuwa manyan jam'iyyun ƙasar, kasancewar suna da jiga-jigai a duka manyan jam'iyun kasar.
Gwamnan jihar mai barin gado Nyesom Wike wanda ya nemi takarar shugabancin ƙasar karƙashin Jam'iyyar PDP na samun goyon bayan wasu gwamnonin jihar huɗu waɗanda ƙarara suke adawa da ɗan takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar tasu.
Kuma a yanzu ana zargin zai mara wa ɗan takarar APC Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen da ke tafe.
To sai dai mista Wike na ci gaba da goyon bayan jam'iyyar PDP a matakin jiha, inda yake goyon bayan ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar.
Kuma da yawa daga cikin al'ummar jihar na da irin wannan ra'ayi, inda suke da niyyar zaɓar jam'iyyu daban-daban a matakin gwamna da na shugaban ƙasa.