Wane ne JD Vance, wanda Trump ya zaɓa a matsayin mataimakinsa?

Asalin hoton, Reuters
Donald Trump ya sanar da sanata JD Vance a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen Amurka na 2024.
Trump ya sanar da mataimakinsa ne a kafarsa ta sada zumunta a ranar Litinin.
"Bayan tattaunawa mai tsawo da dogon nazari kan wanda ya fi dacewa daga cikin mutane da dama, na yanke shawara, wanda ya fi dacewa da zama mataimakin shugaban kasar Amurka shi ne Sanata JD Vance daga jihar Ohio, kamar yadda Trump ya wallafa a kafarsa ta Truth.
Mr Vance ya taɓa caccakar Trump kuma yanzu ya zama wanda zai yi masa mataimaki a zaben shugaban kasa na watan Nuwamban 2024 a Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Wane ne JD Vance?
"Ban taɓa son Trump ba. Bai taɓa burge ni ba."
"Wannan wane irin sakarai ne."
"Ina kallon sa a matsayin abin ƙyama."
Waɗannan wasu daga cikin kalaman JD Vance ne a wasu daga cikin tattaunawa da aka yi da shi, da kuma a shafin Tuwita a 2016, lokacin da wata maƙala da ya wallafa mai taken Hillbilly Elegy ta sa aka san shi a duniya.
Ƴan shekaru bayan haka, Mista Vance ya sauya, inda ya koma ɗaya daga cikin sanannun na kusa da Donald Trump.
Sannan bayan wasu ƴan shekarun, yanzu Vance, wanda sanata ne a karon farko daga Ohio zai kasance tare da Donald Trump a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Kuma za a iya hasashen cewa shi ne zai zama na gaba-gaba cikin waɗanda za su nemi takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar Republican a shekarar 2028.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Asalin sunan Mista Vance shi ne James David Bowman, wanda aka haifa a garin Middletown da ke jihar Ohio a shekarar 1984.
Mahaifiyarsa ta riƙa fama da matsalar shan ƙwaya, yayin da mahaifinsa ya watsar da iyalan nasa a lokacin da JD Vance yake ƙarami.
Kakanninsa na ɓangaren uwa ne suka riƙe shi a lokacin girmansa.
Vance ya yi aiki da zaratan sojojin ƙundunbala na Amurka, waɗanda ake kira Marines, na tsawon shekara huɗu.
Ya yi yaƙi a Iraqi kafin daga baya ya tafi Jami'ar Jihar Ohio, inda ya samu digiri kan kimiyyar siyasa da falsafa.
Daga nan ne kuma ya tafi Kwalejin aikin lauya na Yale, daga nan kuma ya rubuta wani littafi kan rayuwa, wanda ya yi wa take Hillbilly Elegy, littafin da ya samu matuƙara karɓuwa.
A 2017, Vance ya koma Ohio daga California, inda yake aiki sannan kuma ya kafa tasa sana'ar.
A shekarar 2021 Vance ya fara shiga harkar siyasa a matsayin ɗan takarar sanata.
Jim kaɗan bayan shiga fagen siyasa, Vance ya sauya lafuzzansa game da Donald Trump, inda ya nemi afuwa game da bayyana Trump da ya yi a matsayin "abin ƙyama" a baya, sannan kuma ya riƙa nanata kalaman Trump kan zargin maguɗi a zaɓen 2020.
JD Vance ya samu nasarar zama sanata bayan Trump ya goyi bayansa, kuma tun daga wancan lokaci ya zamo ɗaya daga cikin ƴan siyasa da aka fi jin muryarsu a Amurka.










