Martinelli ya saka hannu kan zai ci gaba da taka leda a Arsenal

An wallafa

Dan wasan Arsenal, Gabriel Martinelli ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Emirates.

Dan kwallon Brazil, mai shekara 21 ya koma Emirates daga Ituana ta Brazil a kakar 2019, wanda kawo yanzu ya buga karawa 111 a dukkan fafatawa.

Dan wasan na taka rawar gani a Arsenal a kakar nan, wanda ya ci kwallo bakwai da suka taimaka kungiyar ke matakin farko a Premier League.

Arsenal tana ta daya a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu mai rike da kofin.

Martinelli ya buga wa tawagar Brazil ta matasa 'yan kasa da shekara 23 wasa takwas daga nan ya koma yi wa babbar tawagar tamaula a Maris din 2022.

Yana cikin 'yan kwallon da suka buga wa Brazil gasar kofin duniya a Qatar, wanda ya yi karawa biyu.

Brazil ta kai zagayen quarter finals ne a gasar da Argentina ta lashe na uku jumulla.