Arsenal ta amince za ta sayi Zinchenko daga Man City

An wallafa

Arsenal ta amince da farashin fam miliyan 30 daga Manchester City, domin sayen Oleksandr Zinchenko, ciki har da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan biyu.

Wanda ya buga wasanni da dama a matakin mai tsaron baya daga gefen hagu a kungiyar Etihad, yanzu haka yana tare da 'yan wasa a Amurka wajen atisayen tunkarar kakar bana.

Ana sa ran dan kwallon tawagar Ukraine, mai shekara 25, zai koma Ingila domin kammala cinikin nan da 'yan kwanaki.

Zinchenko yana daga 'yan kwallon da Pep Guardiola ya fara dauka a City a 2016.

Dan wasan ya lashe Premier League hudu da FA Cup da League Cup hudu, bayan wasa 128 da ya yi wa kungiyar.

Zinchenko zai zama na biyu da zai koma Gunners da taka leda a bana, bayan Gabriel Jesus da ya koma Emirates kan fam miliyan 45 a watan jiya.