Haɗarin takaddama tsakanin Najeriya da ƙasashen waje kan batun tsaron ƙasar

An wallafa

Masana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da takaddamar da ta kaure tsakanin Najeriya da wasu ƙasashen yamma, ciki har da Amurka game da fargabar harin ta'addanci a Abuja.

A farkon wannan makon ne Amurka ta gargaɗi 'yan ƙasarta cewa da yiwuwar a kai harin ta'addanci a kan babban birnin Najeriyar. 

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta, tana cewa babu gaskiya a cikin maganar.

Amma daga bisani wasu ƙasashen yammacin duniyar kusan biyar duka sun gargadi mutanensu da su kwana cikin shiri.

Masana harkar diflomasiyya dai na ganin cewa irin wannan katse hanzari ko ƙaryatawa da Najeriya ta yi wa Amurka ka iya shafar dangatar da ke tsakaninsu.

'Wannan gargaɗi ba abin mamaki ba ne'

Masana harkokin tsaro irinsu Barista Bulama Bukarti da Kabiru Adamu na ganin cewa akwai bukatar mahukuntan Najeriya su dau gargaɗin wadannan kasashen ketare gudun kar a makara.

Masanan na da ra'ayin cewa wannan lokaci ba na ce-ce-ku-ce ba ne, da batun da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ana kambama batutuwan da suka shafi tsaron kasarta.

Barista Bulama Bukarti na cibiyar bincike ta Tony Blair da ke Birtaniya ya ce wadannan kasashen da suka ba da gargadi na samun bayanan sirri da suka saba tattarawa kan kungiyoyi ta’addanci.

"Wannan ba abin mamaki ba ne ganin cewa irin wadannan kasashe musamman Amurka na da ƙwarewa a tattara irin wadannan bayanan sirri."

Ya bayar da misali da abin da ke faruwa a Ukraine, lokacin da Amurka ta rinka gargadin cewa Rasha na shirin kai hari, duk da cewa sun musanta ai daga karshe kowa ya ga abin da ya faru, in ji Bukarti.

Sannan masanin ya ce irin wadannan kasashe na samun bayanan sirri masu karfi da ke tabbatar da shirin kai irin wadannan muggan hare-hare a sassan Najeriya da babban birni kasar, Abuja da kewayenta.

Sai dai a nasa ra'ayin Kabiru Adamu, shi ma wani mai ƙwarewa kan lamuran tsaron na cewa kafin duk wani ofishin jakadanci ya fitar da irin wannan bayani game da tsaron ƙasar da yake ciki, ya kamata ya tattauna da hukumomin tsaron ƙasar a kan duk wani bayani da ya tattara.

Ya bayyana cewar wannan bayanai masu karo da juna da ke fitowa tsakanin ɓangarorin biyu sun nuna cewa ofisoshin jakadancin ba su bi matakan da suka kamata ba kafin fitar da bayanan nasu.

Me ya sa mahukunta Najeriya ke cewa ana kambama batun tsaro?

Masanan dai na ganin cewa bai kamata mahukuntan Najeriya su yi biris da wannan gargaɗi ba, ko sanya siyasa a ciki saboda ankarar da mutum ba laifi ba ne.

Bulama Bukarti ya bayar da misali cewa ai wannan gargadi ba sabo ba ne, saboda ko shi kansa ya sha irin wadannan hasashe kuma sai daga baya ya tabbata.

Sannan ya ce bai yi mamaki wannan barazana ba, saboda kungiyoyin ta’addanci musamman Boko Haram sun saba irin wadannan shiri idan suka fahimci irin wannan lokaci na siyasa.

"Boko Haram na yin duk mai yiwuwa domin matsa ƙaimi da kai hare-hare don kawo tasgaro ga zaben Najeriya.

"Ya kamata gwamnatin Najeriya ta gode wa wadannan bayanai ta kuma dau matakai masu karfi don tabbatar da cewa hakan bai faru ba".

Shi ma Kabiru Adamu na da ra’ayi cewa bai kamata a rinƙa samun takun-saƙa tsakanin ƙasa da ƙasa ba kan irin waɗannan shawarwari da ofisoshin jakadanci ƙasashe ke fitarwa.

Illar jayayya kan batun da ya shafi tsaro

Masana na da ra’ayin cewa idan aka ci gaba da siyasatar da wannan batu, nan gaba idan Amurka da ƙawayenta suka samu irin wadannan bayanai to za su rufe bakinsu, su ƙi sanar da gwamnatin Najeriya.

Kuma lokacin da aka ɓata wajen jayayya ko ka ce-na ce kan wannan batu, ya isa a ce, an yi bincike kan barazanar domin maganceta.

"Idan ana musanta irin wadannan bayanai, kamar ana sanar da ‘yan ta’adda da ke shiri, cewa ba a san me suke ciki ba ko iya aikatawa, kuma idan ka samu bayanai a kansu ba za ka yi aiki da su ba.

"Babu gazawa a bangaren gwamnati idan suka ce sun karɓi wadannan bayanai kuma suka yi bincike.

Babu wata riba da Amurka za ta samu da sunan karya da irin wadannan bayanai."