Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na samun zawarawa, Barcelona za ta dauke Arteta, Chelsea na son Trossard
A shirye Chelsea take ta fara tattaunawa da dan wasan gaba na Belgium Leandro Trossard, wanda kwantiraginsa da Brighton zai kare a bazara mai zuwa.
Kungiyar kasar Saudi Arabia Al-Hilal na duba yuwuwar zawarcin Cristiano Ronaldo, bayan da aka raba gari tsakaninsa da Manchester United.
Ita kuwa Real Madrid cewa ta yi ba zai dace da tsarinta na wasa ba a ce ta sake dawo da Ronaldon a karo na biyu.
Shi kuwa dan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva yana ganin abokin wasansa a tawagar Portugal har yanzu yana iya taka leda a babbar gasa bayan da ya kafa tarihi a gasar Kofin Duniya.
Ana ganin Ronaldon da babban abokin hamayyarsa Lionel Messi, ka iya aiki tare wajen yi wa Saudi Arabia fafutukar sama mata damar karbar bakuncin gasar cin Kofin Duniya a 2030, kasancewar ana ganin wannan ita ce gasar duniya ta karshe ta ‘yan wasan biyu.
Mai katafaren kamfanin nan na tufa da sauran kayan kawa, Zara, Amancio Ortega, na sha’awar sayen Manchester United.
Haka shi ma katafaren kamfanin waya da sauran kayayyakin fasaha, Apple na sha’awar sayen United a kan fam biliyan 5.8.
Kamfanonin da ke son sayen kungiyar ta Old Trafford sun tunkari tsohon mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward domin ya kasance wanda za su tuntuba ko shiga tsakani a cinikin.
Inter Milan ta tsawaita kwantiragin Romelu Lukaku, da karin shekara daya.
Hankalin Arsenal ya tashi a kan yadda za su iya ci gaba da rike kociyansu Mikel Arteta, dan Sifaniya ganin cewa Barcelona na harin dauke tsohon matashin dan wasan nata domin zama kociyanta a nan gaba.
Dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, ya ce gasar Kofin Duniya za ta iya taimaka masa ya sake samun sabon kwantiragi da Juventus, inda zamansa zai kare yanzu a bazara ko kuma ya samu tafiya wata kungiyar.
Kungiyoyi da yawa a yanzu na ganin matashin dan wasan Jamus na Borussia Dortmund Youssoufa Moukoko, mai shekara 18, zai bar kungiyar idan kwantiraginsa na yanzu ya kare a karshen kaka.
Aston Villa na zuba ido a kan mai tsaron ragar Sevilla da tawagar Morocco Yassine Bounou.
Watakila dan wasan Real Madrid Rodrygo, na Brazil sai ya biya fam miliyan 6 kudin raba gari da wakilinsa Nick Arcuri.
Barcelona na neman mayar da hankali kan sabunta kwantiragi da kwararrun matasan ‘yan wasanta mai makon sayen sababbi a karshen shekaran nan.
Newcastle za ta yi gogayya da Barcelona wajen zawarcin matashin dan wasan tsakiya na Vasco da Gama Andrey Santos na Brazil mai shekara 18.
Paris St-Germain na duba yuwuwar barin filin wasanta na Parc des Princes ta koma filin wasan na kasa baki daya na Faransa, Stade de France.