Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Qatar 2022: Portugal ta doke Ghana a wasan da Ronaldo ya kafa tarihi
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta doke ta Ghana 3-2 a karawar farko da suka yi a Rukunin H a Gasar Kofin Duniya ta 2022 da ake yi a Qatar.
Ghana ce tawagar Afirka ta farko kuma tilo da ta zira ƙwallo a raga zuwa yanzu a wannan gasar, bayan Kamaru da Senegal da Maroko da Tunisiya sun gaza yin hakan.
Tauraron ɗan wasa kuma kaftin ɗin Portugal Cristiano Ronaldo ne ya ci ƙwallon farko daga bugun finareti a minti na 65, kafin Andre Ayew ya farke ta a minti na 73.
Zuwa minti na 78 Félix Sequeira ya ƙara saka Portugal a gaban Ghana, kafin Conceição Leão ya ƙara ta uku. Ana saura minti ɗaya lokacin wasa ya cika Bukari ya rage wa Ghana yawan ƙwallayen.
Ghana za ta kara da Koriya ta Kudu a wasa na gaba ranar 28 ga watan Nuwamba, inda Portugal za ta kara da Uruguay.
Ronaldo ya sake kafa tarihi
Zaƙaƙurin ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya zama ɗan ƙwallo na farko da ya zira ƙwallo a raga a Gasar Kofin Duniya biyar da ya halarta.
Ronaldo mai shekara 37 ya ci ƙwallo a gasannin 2006, da 2010, da 2014, da 2018, da kuma 2022.
Ƙwallon da ya ci a bugun finareti a wasansu da Ghana, ita ce ta 118 da ya ci wa ƙasarsa Portugal, wanda shi ne kan gaba a ci wa tawagar ƙasa ƙwallaye a duniya baki ɗayanta.
Babban abokin hamayayyarsa Lionel Messi ya ci ƙwallo ne a gasa huɗu. Sauran da suka ci a gasar huɗu su ne Miroslav Klose na Jamus, da Pele na Brazil, da Uwe Seeler na Jamus.