An cire Naomi Osaka daga Qatar Open, Iga Swiatek ta tsallaka zagaye na gaba

..

Asalin hoton, Yahoo

An wallafa

'Yar wasan Tennis ta ɗaya a duniya Iga Swiatek ta ci gaba da jan zarenta a wasannin Qatar Open, yayin da aka yi waje da 'yar ƙasar Japan Naomi Osaka daga gasar da ke gudana a Doha.

Swiatek ta samu nasara ne kan 'yar ƙasar Belarus kuma wadda ta taɓa zama ta ɗaya a duniya, Victoria Azerenka da ci 6-4 da 6-0, wasan da aka kammala cikin mintina 74.

'Yar ƙasar Poland ɗin wadda ta yi nasara a wasanni 11 a Doha, za ta fafata da Karolina Pliskova a wasan kusa da daf da na ƙarshe.

Czech Pliskova ta kawo ƙarshen ƙoƙarin da Osaka ke yi na kusan shekara biyu, inda ta doke ta da ci 7-6 (8-6) 7-6 (7-5).

Osaka gwarzuwar gasar tennins karo huɗu ta dawo wasa ne a watan jiya bayan ta haifi 'yarta Shai a watan Yulin bara.

Wasan da ta buga na kusa da na ƙarshe da Pliskova shi ne wasa mafi nisa da ta buga a wata gasa tun wasan ƙarshe da ta buga a Miami Open a watan Afrilun 2022, inda ta yi rashin nasara a hannun Swiantek.

Pliskova wadda ta lashe gasar WTA ta farko shekaru hudu da suka gabata a Transylvania Open a ranar Lahadi, ta fara shan wuya a hannun Osaka a farkon wasan amma daga baya ta yi maza ta dawo cikin wasan kuma ta yi nasara.