Eric Dier na dab da komawa Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan ya zama baya buga wasa a Spurs tun bayan zuwan sabon kocinta Ange Postecoglou, kuma ya zuwa yanzu wasanni huɗu kacal ya buga wa ƙungiyar.
Tottenham na dab da kammala ɗaukar dan wasan Genoa na baya Radu Dragusin kan kuɗi fan miliyan 25.
Dier zai haɗu da tsohon abokin wasansa a Tottenham Haryy Kane a ƙungiyar da ta lashe gasar Bundesliga 32.
A yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, kocin ƙungiyar Thomas Tuchel ya ce, "shi ɗan wasan baya ne na daban, ya buga lamba shida a Premeir, amma yanzu baya bugawa.
"Za mu saye shi ne domin buga mana baya a matsayin tsakiya, zai iya buga lamba biyu ko uku duka a bayan."
Dier, wanda wata shida ne ya rage a kwantaraginsa da Tottenham a yanzu, ya bugawa Ingila wasa 49 amma yana ta fama da yadda zai samu wuri a ƙungiyarsa a wannan kakar.
Postecoglou ya ce babu damuwa indan Dier ya bar ƙungiyar duk da cewa akwai masu fama da rauni a bayan Spusr ɗin.
Dier ya koma Spurs daga ƙungiyar Sporting Lisbon ta Portugal a 2014 ya kuma buga mata wasannin Premier 274, amma wasa ɗaya aka fara da shi a wannan kakar.
Tottenham da ke matsayi na biyar a Premier za ta buga wasanta na gaba ne a ranar 14 ga watan Janairu da Manchester United.
Bayern Munich na matsayi na biyu a Bundesliga, tana bin bayan Bayern Leverkusen da maki hudu, sai dai tana da kwantan wasa guda a hannu, a hanƙoron da take na lashe gasar sai 12 a jere.











