PSG ta ba Mbappe damar tafiya Liverpool, Busquets ya ki hadewa da Ronaldo

Asalin hoton, AFP
Paris St-Germain ta shirya barin Kylian Mbappe, ya tafi Liverpool a bazarar da ta wuce, amma kuma dan wasan na Faransa ya ki tafiya saboda rade-radin da ake yin a dangnta shi da Real Madrid. (Athletic)
Arsenal ba za ta tashi hankalinta wajen sayen ‘yan wasa ba a watan Janairu bayan da Chelsea ta yi mata shigar sauri ta saye Mykhailo Mudryk, dan Ukraine mai shekara 22, maimakon haka za ta jira sai a bazara ta nemi dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice. (Sun)
West Ham ta yi kokarin daukar aron dan bayan Ingila Harry Maguire, amma kuma kociyan Manchester United Erik ten Hag, wanda ba ya son rabuwa da kyaftin din kungiyar tasa har zuwa karshen kaka ya ki. (Mail)
Watakila Everton ta nemi maye gurbin kociyanta Frank Lampard, mai shekara 44, da tsohon kociyanta David Moyes, mai shekara 59, duk da cewa Moyes din shi kansa yana fuskantar barazanar rasa aikinsa a West Ham. Dukkanin kungiyoyin biyu na matakin faduwa daga Premier. (Sun)
Moyes zai iya rasa aikin nasa idan West Ham ta yi rashin nasara a hannun Everton a filin wasa na London ranar Asabar. (Telegraph)
Manchester United ta kara kudi a tayin matashin dan wasan Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 18, bayan da Real Madrid ta nuna sha'awarta a kansa. (Independent)
Dan bayan Barcelona da Sifaniya, Sergio Busquets, ya yi watsi da tayin kwantiragi mai tsoka na biyansa albashin fam miliyan 17 a shekara daga kungiyar Cristiano Ronaldo ta Saudiyya, Al Nassr. (Catalunya Radio, ta Mail)
Bayanai na nuna cewa Fulham na sha'awar tsohon dan wasanta na gaba Josh Maja, mai shekara 24, da take son saye a kan fam miliyan 4. Dan Najeriyar haifaffen London wanda ya yi zaman aro a Craven Cottage a 2021, ya ci bal 11 a wasa 19 da ya yi wa Bordeaux a gasar Faransa ta Ligue 2 a bana. (Sun)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Chelsea da Manchester United na shirin gogayya da Tottenham wajen sayen golan Brentford David Raya, dan Sifaniya a bazaran nan. (Telegraph)
Tottenham ta yi tayin bayar da fam miliyan 30 da sauran 'yan tsarabe-tsarabe a kan dan bayan Sporting Lisbon Pedro Porro, dan Sifaniya , amma kuma kungiyar ta Portugal tana son sai kungiyar ta arewacin London ta biya ainahin kudin sayar da shi a kwantiragi fam miliyan 39. (Record)
Atletico Madrid na shirin sayen dan gaban Barcelona na Netherlands Memphis Depay a kan fam miliyan 2.6. (Fabrizio Romano)
FC Copenhagen ta tabbatar da tattaunawa tsakaninta da Leicester City a kan dan bayan Denmark Victor Kristiansen, amma kuma ta ce ba tabbacin cinikin zai fada. (Leicester Mercury)
Dan Ronaldinho Joao de Assis Moreira na halartar gwaji a tsohuwar kungiyar mahaifinsa Barcelona. Sai dai zuwa yanzu matashin dn wasan mai shekara 17 bai burge jami'an kungiyar ba amma shugabanta Joan Laporta ya bukaci a kara masa lokaci. (La Gazzetta dello Sport, ta Mail)
West Ham ta taya dan wasan Aston Villa Danny Ings, na Ingila da nufin karfafa gabanta yayin da take fuskantar barazanar faduwa daga Premier. (Telegraph)












