Real Madrid da Barcelona za su ƙaurace wa taron La Liga a Dubai

Barca da Real

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona da Real Madrid ba za su halarci taron ƙungiyoyin gasar La Liga da aka shirya za ayi a Dubai a mako mai zuwa.

Kungiyoyin biyu an sanar da su taron a wata wasika a ranar 25 ga watan Nuwamba kan cewar za a tattauna sauye-sauye kan dokokin gasar.

Sai dai sun ce ba za su tura wakilai ba a taron da za a yi a ranar 7 ga watan Disamba.

Barca da Real na daga cikin kungiyoyi 12 da suka nemi a shekara ta 2021 a kirkiro da wata gasar mai suna European Super League (ESL).

Amma bukatar ta fuskanci cikas.

A wata sanarwa, Madrid ta bayyana taron na La Liga a matsayin "haramtacce".

"Babu wata hujja a kira taron gaggawa ba tare da an zauna an yi mahawara kan tsare-tsaren La Liga ba," in ji Madrid.

Ita ma Barca ta ce "Matsayin FC Barcelona shi ne a cimma yarjejeniya bayan an tattauna a kan lokaci a kan batutuwa."