Makomar Man United na hannun Bayern Munich a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Galatasaray da Manchester United sun tashi 3-3 a wasa na biyar-biyar a rukunin farko na gasar Champions League ranar Laraba.

Manchester United ce ta fara cin kwallo ta hannun Alejandro Garnacho a minti na 11 da fara wasa, sannan Bruno Fernandes ya ci na biyu minti bakwai tsakani.

Daga baya ne Galatasaray ta farke daya ta hannun Hakim Ziyech daga nan suka je hutu, United na cin 2-1.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Scott McTominay ya ci wa United kwallo na uku.

Sai dai kuma Galatasaray ta zare biyun ta hannun Hakim Ziyech da kuma Kerem Akturkoglu.

Yanzu makomar Man United ta koma hannun Bayern Munich waɗanda za su buga wasan ƙarshe a rukunin a Ingila.

Kawo yanzu an zura kwallo 33 a ragar Man United a dukkan fafatawa 20 da ta yi a bana.

Ta zama ta farko da aka dura wa kwalllaye tun bayan 1962/63, bayan da 43 suka shiga ragarta a dukkan fafatawa a irin wannan lokacin.

Koda yake ba a buga wasan Bayern Munich da Copenhagen ba, amma Bayern tana ta daya da maki 12, sai Galatasaray ta biyu da maki biyar, Copenhagen ta uku da maki huɗu, iri ɗaya da na United da take matakin ƙarshe.

Ranar 12 ga watan Disamba za a buga wasa na karshe a cikin rukuni na farko, inda Manchester United za ta karbi bakuncin Bayern Munich a filin wasa na Old Trafford.