Hukumonin United sun goyi bayan Ten Hag

Eric Ten hag

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumomin Manchester United sun fito fili sun ƙaryata iƙirarin cewa suna nazarin zaɓin da suke da shi na sauya koci Eric Ten Hag.

Ten Hag zai yi farin cikin wannan goyan bayan, amma ya san wasanni masu zuwa da Fulham da FC Copenhagen da kuma Luton suna da matuƙar muhimmaci a gare shi, saboda idan bai yi nasara ba shugabannin United za su fuskanci babban matsin lamba don yin canji.

Ana raɗe -raɗin cewa cikin waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin Ten hag sun haɗa da kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim da kuma tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane.

United ba ta yi rashin nasara a hannun Fulham ba tun shekarar 2009, kuma tana buƙatar aƙalla canjaras ko kuma nasara daga tafiyarta zuwa Denmark don ci gaba da fatan kai wa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai kuma tun 1897 ba ta yi rashin nasara a gida da Luton ba.