Wa zai taka rawar gani a kakar Premier League ta 2022/23

An wallafa

Ranar Juma'a 5 ga watan Agustan 2022 za a fara gasar Premier League ta bana kakar 2022/23 ta 124 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Manchester City ce mai rike da kofin kuma biyu a jere da ta lashe wato a 2020–21 da kuma ta 2021–22.

Mohammed Abdu ya hada bayanai kan wasannin 2022/23

A kakar bana ta tamaula da za a fara ta 2022–23, kungiyoyin za su iya sauya 'yan wasa biyar maimakon uku da ake yi a baya.

Za a iya sauya 'yan wasa uku a minti 45 din farko, sannan a saka sauran a zagaye na biyu, domin a rage bata lokaci idan ana taka leda.

Wannan shi ne karon farko da za a fara canja 'yan kwallo biyar a Premier League, bayan da tuni Bundesliga da Ligue 1 da Primeira Liga da La Liga da kuma Serie A suka dade da tsarin.

Haka kuma a kakar nan za a buga gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci tsakanin Nuwamba zuwa cikin Disambar 2022.

Saboda haka za a yi hutu a Premier a makon12 ko 13 ga watan Nuwamba zuwa 26 ga watan Disambar, domin babbar gasar tamaula ta cin kofin duniya.

'Yan wasa za su daina sa gwiwa daya a kasa kafin fara tamaula

Kyaftin-kyaftin din kungiyoyin Premier League sun amince cewar ba duk wasa ne za su ci gaba da sa gwiwa daya a kasa ba daga kakar nan, don goyon bayan yaki da wariwar launin fata.

An dai amince cewa za a iya yi a farkon bude gasar ko lokacin rufe ta ko wani babban wasa a Ingila, shima ba wai ya zama wajibi ba.

Sai dai kuma kungiyoyin sun yi kira da babbar murya cewar suna yaki da wariyar launin fata da duk wani nau'in cin zarafi a fannin taka leda.

Kungiyoyi 20 ne ke buga gasar

Kungiyoyi 20 ke buga gasar Premier League, inda 17 daga bara za su hadu da ukun da suka samu gurbin fafatawa a kakar bana daga Championship.

Wanda suka hauro zuwa Premier League sun hada da Fulham, wadda ta yi kaka daya rabonta da gasar da Bournemouth kaka biyu rabonta da wasannin da Nottingham Forest, wadda shekara 23 rabonta da Premier League.

Gibin shekara 23 rabon da kungiya ta koma buga Premier League da Nottingham ta yi shi ne har yanzu mai tsawo a tarihi da ake da shi, bayan barin gasar.

Kungiyoyi ukun sun maye gurbin Burnley, wadda ta yi kaka shida a Premier League da Watford da kuma Norwich City, wadanda suka yi kaka daya a wasannin da aka karkare a bara.

 

Da yake ranar 5 ga watan Agusta za a fara kakar wasan Premier League ta 2022/23, inda za a fara da kece raini tsakanin Crystal Palace da Arsenal a Selhust Park.

Tuni kungiyoyi 20 da za su fafata a kakar bana suka daura aniyar yadda za su taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Wasu da dama sun sayo sabbin 'yan wasa don kara bunkasa kwazonsu, yayin da wasu suka buga wasannin sada munta.

A bana Nottingham Forest wadda rabon da ta buga Premier League tun bayan shekara 23, ita ce kan gaba da ta dauki yan kwallo 13 kawo wannan lokacin.

Leicester City ce kawo yanzu ba ta sayi dan kwallo ko daya ba, watakila ta dauka nan gaba.

Ranar Asabar Liverpool ta doke Manchester City 3-1 ta lashe Community Shield, daga nan an buga gangar tunkarar kakar bana kenan.

Manchester City ce ta lashe Premier League a 2021/22 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool a ranar karshe da aka rufe wasannin.

Jadawalin wasannin makon farko

Ranar Juma’a 5 ga watan Agusta

  • Crystal Palace  da Arsenal

Ranar Asabar 6 ga watan Agusta        

  • Fulham da Liverpool         
  • Leeds United da Wolverhampton Wanderers          
  • Newcastle United da Nottingham Forest
  • Tottenham da Southampton 
  • Bournemouth da Aston Villa      
  • Everton da Chelsea

Ranar Lahadi 7 ga watan Agusta        

  • Manchester United da Brighton & Hove Albion       
  • Leicester City da Brentford    
  • West Ham United da Manchester City

Karawa tsakanin Crystal Palace da Arsenal

Za a bude gasar bana da wasan hamayya tsakanin kungiyoyin birnin Landan Crystal Palace da Arsenal da za su kece raini a Selhurst Park ranar Juma'a 5 ga watan Agusta.

Kamar Arsenal a bara ta yi wasan farko da kungiyar birnin Landan Brentford, sannan ta yi rashin nasara da ci 2-0 a karawar.

Me kuka sani kan wasan Palace da Gunners?

Crystal Palace ta yi rashin nasara a wasa daya daga takwas da ta kara da Gunners a Premier League da canjaras biyar da cin wasa biyu.

Palace na sa ran doke Arsenal a jere a karon farko a tarihin haduwarsu.

Arsenal ta yi rashin nasara a wasan farko da buge Premier League karo biyar a fafatawa tara baya da yin nasara a hudu.

Wasa biyar kacal Palace ta yi nasara daga 22 a wasan farko na bude Premier League da canjaras 7 da rashin nasara a fafatawa 10.