Najeriya ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasar mata ta Kofin Duniya

Esther Onyenezide

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Najeriya 'yan kasa da shekara 20 ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasar kofin duniya a Costa Rica, bayan da ta ci Koriya ta Kudu 1-0.

To sai dai Ghana ba za ta kai zagayen gaba ba a wasannin, bayan da ta kara shan kashi a wasa na biyu a rukuni na hudu.

Wasan na rukuni na uku da Falconets ta buga an samu tsaikon awa daya kafin a fara, bayan da guguwa da iska da zubar ruwan sama ya mamaye filin wasa na Alejandro Morera Soto.

Tun kan hutu Koriya ta Kudu ta yi ta kai hare-hare ga ragar Nageriya, amma haka suka je hutu ba ci.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Falconets ta kara kwazo, inda saura minti bakwai a tashi daga karawar Esther Onyenezide ta ci kwallo.

Falconets wadda ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Jamus a gasar 2010 da kuma 2014 ta fara da cin Faransa 1-0 a wasan farko a rukuni na uku.

Ranar Alhamis Najeriya za ta fuskanci Canada a wasa na uku kuma na karshe a rukunin da Canada, wadda ta sha kashi a wasa biyu da ta kara.

Ghana daya daga cikin mai wakiltar Afirka ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Japan a wasa na biyu a rukuni na hudu.

Ghana wadda ba ta haura wasannin cikin rukuni a karo na biyar da take halartar wasannin kofin duniya, za ta buga da Nertherlands ranar Alhamis.