Ana alakanta Ronaldo da tafiya Inter Miami, Barcelona na zawarcin Dalot

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An yi wa dan wasan Portugal mai shekaru 37 da ke buga tsakiya Cristiano Ronaldo, tayin samun daman raba gari da Manchester United ta hanyar tafiya Inter Miami, kungiyar tsohon abokinsa a harkar tamaula David Beckham. (Star)

Mai tsaron raga a Denmark, Kasper Schmeichel ɗan shekara 35, na iya sake sauya kungiya a cinkin ‘yan kwallo ta watan Janairu, wata shida kenan da barowarsa Leicester.(L'Equipe via Leicester Mercury)

Kungiyar Barcelona da ke zawarcin ɗan wasan baya na farautar ɗan wasan Manchester United Diogo Dalot, mai shekara 23. (Sport)

Leeds United ta cimma yarjejeniya da Cody Gakpo inda yanzu suke tattaunawa kan kudin da za ta bai wa PSV Eindhoven kan ɗan wasan mai shekara 23.(Mirror)

Southampton na farautar ɗan wasan Celtic, Filipe Jota, mai shekara 23. (Football Insider)

Liverpool ta shiga sahun wadanda suka yi zawarcin ɗan wasan Mali, Yves Bissouma, mai shekara 26, a karshen kaka kafin ya koma Tottenham daga Brighton.(The Athletic)

Paris St-Germain na duba hanyoyi dawo da ɗan wasanta Adrien Rabiot, mai shekara 27, da kwantiraginsa ke kan karewa Juventus. (Fichajes)

Arsenal ta fuskanci babban koma baya wajen cefanan ɗan wasan Juventus mai shekara 24, Manuel Locatelli, bayan ɗan wasan asalin Italiya ya zabi ya zauna a Turin. (Football London)

Manchester United na Shirin ganawa da wakilan Alejandro Garnacho mai shekara 18 ɗan Argentina. (AS via Sport Witness)

Dan wasan Roma Tammy Abraham, ya ki nuna ba lallai ya sake dawowa Chelsea ba a nan gaba.(90 Min)